Kujerar Shugaban Kasa: Makarfi ya samu goyon bayan Jam'iyyar PDP reshen Jihar Kaduna a Zaben 2019

Kujerar Shugaban Kasa: Makarfi ya samu goyon bayan Jam'iyyar PDP reshen Jihar Kaduna a Zaben 2019

Da sanadin shafin jaridar Daily Trust mun samu rahoton cewa, a ranar Litinin din da ta gabata ne jam'iyyar PDP reshen jihar Kaduna ya karfafa amincin ta tare da goyon bayan kudirin kujerarr Shugaban Kasa na Sanata Ahmad Muhammad Makarfi.

Jam'iyyar ta tabbatar da wannan aminci ne tare da goyon baya a babban ofishin ta dake jihar ta Kaduna bayan gudanar da taron masu da ruwa da tsaki da Sanata Makarfi mai neman takarar kujerar shugaban Kasa.

Kujerar Shugaban Kasa: Makarfi ya samu goyon bayan Jam'iyyar PDP reshen Jihar Kaduna a Zaben 2019

Kujerar Shugaban Kasa: Makarfi ya samu goyon bayan Jam'iyyar PDP reshen Jihar Kaduna a Zaben 2019

Legit.ng ta fahimci cewa, a makon da ya gabata ne tsohon gwamnan na jihar Kaduna ya bayyana kudirin sa na tsayawa takarar kujerar shugaban kasa a zaben 2019.

KARANTA KUMA: Boko Haram: Wani sabon hari ya salwantar da rayukan Mutane 4 da raunata 6 a garin Konduga

Cikin jawaban sa a taron na masu ruwa da tsaki shugaban jam'iyyar reshen jihar Kaduna, Dakta Hassan Hyet ya bayyana cewa, bayyana kudirin Makarfi na tsayawa takara ya yi daidai da lokacin da Najeriya ke bukatar sa sakamakon kasancewar sa Mutum mai hangen nesa.

A sanadiyar haka ne shugaban jam'iyyar ya nemi mambobin ta kan su kara kaimi wajen cimma burin Makarfi na samun nasarar lashe takara ta kujerar shugaban kasa a zaben 2019 duba da hazakarsa ta tabbatar da haduwar kan jam'iyyar sa tsawon shekaru da dama da suka gabata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel