Nigerian news All categories All tags
Zan kawo karshen kashe-kashe idan aka zabe ni shugaban kasa - Makarfi

Zan kawo karshen kashe-kashe idan aka zabe ni shugaban kasa - Makarfi

Tsohon shugaban rikon kwarya na jam'iyyar PDP, Sanata Ahmed Makarfi ya ce zai kawo karshen kashe-kashen da sauran matsalolin tsaro da ke adabar wasu sassan Najeriya muddin aka zabe shi a matsayin shugaban kasa.

Makarfi ya yi furta wannan magana ne a jiya a garin Kaduna bayan wasu jiga-jigan jam'iyyar PDP a jihar sun nuna goyon bayansu ga son tsayawa takarar nasa.

DUBA WANNAN: Karshen duniya: An kama shi turmi da tabarya da matar mahaifin sa

A cewar Makarfi, babu wanda ya fi shi dacewa ya ja ragamar Najeriya musamman idan a kayi la'akari da irin kwarewa da wayewarsa a kan harkokin siyasa da zamantakewar rayuwa.

Zan kawo karshen kashe-kashe idan aka zabe ni - Makarfi

Zan kawo karshen kashe-kashe idan aka zabe ni - Makarfi

A jawabin da ya yi a farko taron, ciyaman din PDP na Jihar, Dr. Hassan Hyet ya ce babu wanda ya fi Makarfi dacewa ya shugabanci Najeriya a shekarar 2019.

Kazalika, Sanata Makarfi da tsohon ministan ayyuka na musamman, Kabiru Turaki sun mika sakon ta'aziyyarsu ga al'ummar jihar Plateau bisa rikicin da ya barke kuma ya yi sanadiyar mutuwar daruruwan mutane ciki har da mata da yara a ranar Lahadi.

Sun koka da rashin ingantaccen tsaro a kasar kuma sunyi kira ga hukumomin tsaro su zage damtse wajen kare rayyuka da dukiyoyin al'umma a kasar.

A wata sanarwar da ta fito daga bakin hadiminsa a fannin yada labarai, Mukhtar Sirajo, Sanata Makarfi ya ce, "duk da cewa ba za a rasa yiwuwar rashin jituwa tsakanin mutane ba, hanyar da ta dace na warware matsaloli shine tattaunawa da juna."

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel