Da duminsa: Rigimar kungiyar mota ya yi sanadiyar mutuwar mutum 3, wasu da dama sun raunata

Da duminsa: Rigimar kungiyar mota ya yi sanadiyar mutuwar mutum 3, wasu da dama sun raunata

An tabbatar da rasuwar mutane uku yayin da wasu da dama suka sami munanan raunuka a wata rikicin shugabanci da ta barke a safiyar yau Talata a tashan mota na Empress Junction da ke karamar hukumar Udu a Jihar Delta.

A yayin da yake tabbatar da afkuwar lamarin ga jaridar Vanguard, mataimakin ciyaman na yankin, Justice Iyasere ya ce lamarin ya afku ne a safiyar yau Talata kuma mutane uku sun rasa rayyukansu yayin da wasu mutanen kuma suna asibiti inda suka karban magunguna.

Da duminsa: Rigimar kungiyar mota ya yi sanadiyar mutuwar mutum 3, wasu da dama raunata

Da duminsa: Rigimar kungiyar mota ya yi sanadiyar mutuwar mutum 3, wasu da dama raunata

KU KARANTA: Ba a taba munafikin shugaban kasa a Najeriya kamar Obasanjo ba - Soyinka

Ya ce: "A yanzu dai kurar da lafa bayan yan sanda da sojoji sun iso wurin da abin ya faru."

A wata labarin kuma, Legit.ng ta kawo muku cewa gwamnatin kasar Amirka ta yi tir da kashe-kashen da a kayi a Jihar Filato inda tayi kira ga shugaba Muhammadu Buhari ya gudanar da bincike tare da hukunta dukkan wadanda aka samu da hannu cikin kashe-kashen don kare afkuwar hakan a gaba.

Amurkan kuma ta mika sakon ta'aziyyar ta ga al'umman da abin ya shafe tare da kira da shugabanin unguwani da masu rike da mukamen siyasa su hada kai wajen ganin mutan sun zauna lafiya.

Kakakin yan sandan jihar Terna Tyopev ya cean kone gidaje 50 da motocci biyu da kuma babura 15 a harin da makiyaya suka kai.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel