Ziyarar Atiku: DSS sun hana yan jarida daga shiga filin jirgin Asaba

Ziyarar Atiku: DSS sun hana yan jarida daga shiga filin jirgin Asaba

Jami’an yan sandan farin kaya (DSS) sun hana yan jarida daukar bayanan isowar tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa PDP a zaben 2019 a filin jirgin sama na Asaba.

Atiku dai zai ziyarci jihar ne don tattaunawa da Gwamna Ifeanyi Okowa kan kudirinsa.

Shugaban DSS wanda ba’a san ko wanene ba zuwa yanzu ya ce “An bamu umurnin cewa kada mu bar yan jarida su shigafilin jirgi domin daukar rahoton isowar Atiku.

“Duk yan jarida su je fadar gwamnati su jira, an bamu umurnin cewa kada mu bari yan jarida su shiga saboda kada su bayar da wani umurni ba tare da saninmu ba.

Ziyarar Atiku: DSS sun hana yan jarida daga shiga filin jirgin Asaba

Ziyarar Atiku: DSS sun hana yan jarida daga shiga filin jirgin Asaba

KU KARANTA KUMA: Yan sanda sun cafke wata mata bayan ta jefa jariri a masai

“Idan ba ku rike mutuncinku ba zan sa jami’aina su yi waje da ku”. Nan take ya sa jami’ai su tura su waje.”

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Atiku Abubakar ya bayar da tallafin naira miliyan 10 ga mutanen da guguwar iska ya cika da su a jihar Bauchi.

A kwanan nan ne dai annobar guguwar iska ya cika da mutanen jihar Bauchi inda ya lalata dukiyoyi, gidaje, makarantu, wuraren kasuwanci, masallatai, da cocina.

Atiku ya bayar da wannan tallafi ne a ranar Litinin, yayinda ya ziyarci sarkin Bauchi, Rilwan Adamu a fadarsa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel