Biafra: Kotu ta bayar da belin yaran Nnamdi Kanu

Biafra: Kotu ta bayar da belin yaran Nnamdi Kanu

- Kowa ya ja ruwa shi ruwa kan daka inji masu iya magana

- 'Dan da kyar, bayan shafe shekaru a tsare an bayar da belin yaran Nnamdi Kanu amma da wahala su iya cika sharrudan

A jiya Litinin ne Alkaliyar wata babbar kotun tarayya dake zamanta a Abuja, mai shari'a Binta Nyako ta bayar da belin wasu mutane hudu da aka kama masu fafutikar samun 'yantacciyar kasar Biafra akan kudi Naira miliyan 10 kowanen su.

Alkaliyar ta bada umarnin sakin Bright Chimezie, Chidiebere Onwudiwe, David Nwawuisdi da kuma Benjamin Madubugwu. Chimezie, Onwudiwe, Madubugwu da Nwawuisi, ana tuhumar su ne da laifin cin amanar kasa da kuma mallakar makamai ba bisa ka'ida ba.

Biafra: Kotu ta bayar da belin yaran Nnamdi Kanu

Biafra: Kotu ta bayar da belin yaran Nnamdi Kanu

Suna tsare tun shekara ta 2016 tare da shugaban su Nnamdi Kanu wanda tun 22 ga watan Satumba 2017 ba'a sake ganinsa ba kuma ba'a san inda ya shiga ba.

KU KARANTA: Dubu ta cika: Wadansu da suka yiwa gawa fyade sannan suka gasa namanta suka cinye sun shiga hannu

Nyako ta ce ta yi duba na tsanaki game da korafe-korafe da kuma uzuri, tare da shekarun da suka ɗiba a tsare ba tare da an yanke musu hukunci ba, kamar yadda lauyoyin wanda ake tuhumar suka nemi a musu afuwa.

Biafra: Kotu ta bayar da belin yaran Nnamdi Kanu

Biafra: Kotu ta bayar da belin yaran Nnamdi Kanu

Ta kara da cewa wasu daga cikin su suna cikin wani yanayi na bukatar kulawar likitoci wannan shi ne dalilin da yasa ta bada belin nasu.

Alkaliyar ta bada belin kowane daga cikin su akan kudi Naira miliyan 10 tare da gindaya sharuda kamar haka; ba a yadda kowanen su ya shiga wani taro domin tattaunawa da shi ba.

Kuma an hana kowane daga cikin su yin tafiya zuwa kasashen ketare sannan kotu ta bukaci su bada passport din su, har wa yau kotu ta hana su yin taro ko magana da yan jarida ko kuma yin taron murnar dawowar su gida, Alkalin tace sabawa daya daga cin wadannan dokoki zai sa kotu ta dawo da su gidan kaso.

Daga karshe kuma Alkalin ta bada umarnin kowanne daga cikin su yake zuwa ofishin shugaban hukumar yan sanda na yankin da yake duk bayan sati biyu domin tabbatar da yana nan bai tsere ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel