Duba kasar da mata suka fi shiga hatsari a duniya

Duba kasar da mata suka fi shiga hatsari a duniya

A wani bincike da gidauniyar Reuters ta yi, ta bayyana kasar Indiya a matsayin kasar da mata suka fi shiga hadari a duniya

Duba kasar da mata suka fi shiga hatsari a duniya

Duba kasar da mata suka fi shiga hatsari a duniya

A wani bincike da gidauniyar Reuters ta yi, ta bayyana kasar Indiya a matsayin kasar da mata suka fi shiga hadari a duniya.

A rahoton da binciken ya fitar ya nuna cewar mata suna fuskantar cin zarafi ta hanyar tsangwama, lalata da kuma kyara a wurin wasu masu dadaddun al’adu, bayan haka bincike ya nuna cewar a kasar ne aka fi safarar mata fiye da ko ina a duniya.

DUBA WANNAN: Karku bar APC, wani jigo a jam'iyyar yana rokon 'yan jam'iyyar karsu juya musu baya

Kasar Afghanistan ita ce kasa ta biyu da kuma kasar Syria a matsayin ta uku a jerin kasashen.

A cikin kasashen yammacin duniya Amurka ce kasa daya tilo da aka ambata a cikin jerin kasashen, wadda ita ce kasa ta 10 a jerin kasashen.

A cewar masu binciken, mata a kasar Amurka suna fuskantar matsin lamba ta hanyar yi musu fyade, kuma ba a basu damar kwato hakkin su.

Gidauniyar Thomas, tace ta tattara bayanan ta a tattaunawar da suka yi da kwararru akan irin harkokin mata su guda 550 a tsakanin watan Maris zuwa watan Mayu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel