Nigerian news All categories All tags
Jam'iyyar PDP tayi kaca-kaca da Fadar Shugaban Kasa kan Kashen-Kashen Jihar Filato

Jam'iyyar PDP tayi kaca-kaca da Fadar Shugaban Kasa kan Kashen-Kashen Jihar Filato

A ranar Litinin din da ta gabata ne jam'iyyar adawa ta PDP ta kalubalanci jawaban fadar shugaban kasa dangane da kisan gillar al'ummar kasar nan da ya afku a jihar Filato, inda ta bayyana cewa akwai rashin tausayi, jin kai da kuma raunin hankali da ya kamata ta nemi afuwar 'yan Najeriya.

Jam'iyyar cikin wata sanarwa da sanadin Kakakin ta, Mista Kola Ologbondiyan ya bayyana cewa, 'yan Najeriya sun sanya idanu kan fadar shugaban domin daukar matakai na gaggawa domin tabbatar da tsaro, kiyaye rayukan mutane, adalci da kuma kawo sauki ciki lamuran wadanda ke fama da ibtila'in hare-hare a kasar nan.

Ko shakka babu abin kunya shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ci gaba da zargi da tuhumce-tuhumce na dora kan wasu 'yan siyasa a madadin tashi tsaye wajen tunkarar matsalolin tsaro da ta'addanci a kasar nan kamar yadda kakakin jam'iyyar ya bayyana.

Jam'iyyar PDP tayi kaca-kaca da Fadar Shugaban Kasa kan Kashen-Kashen Jihar Filato

Jam'iyyar PDP tayi kaca-kaca da Fadar Shugaban Kasa kan Kashen-Kashen Jihar Filato

Hakazalika kakakin jam'iyyar ya bayyana cewa, akwai takaici dangane da yadda gwamnatin shugaba Buhari ta ba da baya ga muhimmancin kisan gillar da ake faman yiwa al'ummar kasar nan da kuma nuna halin ko oho wajen daukar wani mataki don ganin an bankado masu aika wannan mummunan laifi tare da hukunta su.

Ya ci gaba da cewa, wannan yanayi mai matukar ciwa jam'iyyar tuwo a kwarya ya kara haddasa tsoro cikin zukatan mafi akasarin al'ummar kasar nan sakamakon halin ko in kula da gwamnatin ta nuna ga rayuwar su.

KARANTA KUMA: Gangamin APC: Oyegun ya yi jawaban bankwana ma su ratsa jiki

Legit.ng ta fahimci cewa, jam'iyyar ta PDP ta jaddada alhakin kowace gwamnati ne ta tabbatar da tsaro da kuma kariya ga lafiya da rayuwar al'ummar ta gami da dukiyoyin su.

Mista Ologbondiyan ya kara da cewa, gwamnatin shugaba Buhari tayi watsi da nauyin da rataya a wuyanta na bayar da kariya da tsaro ga al'ummar kasar nan inda ya bar makomar su a hannun azzaluman Mahara.

Bugu da kari Kakakin jam'iyyar ya bayyana takaicin sa dangane da yadda shugaba Buhari ya gaza sanya dadadan kalamai cikin jawaban ga al'ummar kasar nan kan afkuwar harin Filato sai dai fusatar da su ta hanyar sharhin hadiman sa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel