Nigerian news All categories All tags
Matashi ne zai zamo shugaban kasa a 2019 – Babban malami

Matashi ne zai zamo shugaban kasa a 2019 – Babban malami

Babban limami kuma shugaban cocin Emmanuel Evangelical Church of God, Prophet Kayode Emmanuel, ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari zai mika mulki ga wani matashi a 2019.

Ya bayyana hakan ne hedkwatan cocin dake Shomolu bayan wani gagarumin addu’a da azumi da suka gabatar mai taken : My Cup Runs Over.

A cewarsa, abunda yan Najeriya ke bukata a wannan lokaci shine hada kai, sannan a ajiye banbancin addini, kabila da siyasa domin yiwa kasar addu’a.

Matashi ne zai zamo shugaban kasa a 2019 – Babban malami

Matashi ne zai zamo shugaban kasa a 2019 – Babban malami

KU KARANTA KUMA: Rasha 2018: Ba ma jin tsoron Messi – Super Eagles

“Mu hadu muyiwa Najeriya addu’a. Daga wahayin da Allah yayi, zai mika mulki ga wani matashi wadda zai yi ayyukan da ake tsammani sannan ya kai kasar zuwa ga mafarkinta. Allah ya shiryawa al’umman kasar da kasar kamar yadda yayi alkawari. Sannan matasa za su lashe zaben gwamnoni daban-daban, indai har za’ayi zabe mai inganci a 2019,” Inji Prophet Emmanuel.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Kola Abiola ya bayyana cewa Mahaifiyar sa Simbiat Atinuke Abiola wanda mai dakin Marigayin ‘Dan siyasar ne ba ta so Abiola ya nemi takarar Shugaban Kasa lokacin Janar Ibrahim Babangida yana mulki ba.

Babban ‘Dan MKO Abiola ne ya bayyana wannan da kan sa kwanan nan inda yace Mahaifiyar ta sa Simbiat Abiola ta ba MKO Abiola shawara ya hakura da neman mulki muddin Janar IBB yana rike da kasar a lokacin mulkin Soji.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel