Nigerian news All categories All tags
Rasha 2018: Ba ma jin tsoron Messi – Super Eagles

Rasha 2018: Ba ma jin tsoron Messi – Super Eagles

Shahararren dan wasan kwallon kafa na Najeriya Abdullahi Shehu ya bayyana cewa basa jin tsoron haduwa da fitaccen dan wasan Argentina Lionel Messi a karawar da za su yi a gasar cin kofin duniya.

Kungiyar Super Eagles dai zata kara da Argentina a yau Talata, 26 ga watan Yuni.

Wasan ne zai tantance makomar kasashen biyu a gasar yayin kowace take neman yin nasara.

Rasha 2018: Ba ma jin tsoron Messi – Super Eagles

Rasha 2018: Ba ma jin tsoron Messi – Super Eagles

Ba wannan ba ne karon farko da kasashen suke haduwa a tarihin gasar, sai dai a baya Argentina ce take samun nasara a dukkannin karawa hudu da suka yi a gasar.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa kungiyar likitocin 'yan wasan kwallon kafa na Super Eagles suna aiki ba dare ba rana domin tabbatar da cewa Mikel Obi ya samu cikakkiyar lafiyar da zai samu damar buga wasan da Najeriya zata yi da kasar Argentina a ranar Talata.

KU KARANTA KUMA: An bayyana wadanda za su kara da Najeriya idan sun yi nasara a Gasar World Cup

A binciken da likitocin suka gabatar ya nuna cewa, dan wasan ya samu karamin rauni a hannunsa a dai-dai lokacin da ake gab da tashi daga wasan da Najeriya ta buga da kasar Iceland inda Najeriya ta lashe wasan da ci 2 a ranar juma'ar nan.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel