Nigerian news All categories All tags
Karku bar APC, wani jigo a jam'iyyar yana rokon 'yan jam'iyyar karsu juya musu baya

Karku bar APC, wani jigo a jam'iyyar yana rokon 'yan jam'iyyar karsu juya musu baya

Dan takarar gwamna kuma shugaban ma'aikatan jihar Imo, Chief Uche Nwosu, ya bukaci yan jam'iyyar APC, wadanda suka kafa wata kungiya mai suna Allied Forces, dake jihar Imo da kada su juya wa jam'iyyar ta APC baya

Karku bar APC, wani jigo a jam'iyyar yana rokon 'yan jam'iyyar karsu juya musu baya

Karku bar APC, wani jigo a jam'iyyar yana rokon 'yan jam'iyyar karsu juya musu baya

Dan takarar gwamna kuma shugaban ma'aikatan jihar Imo, Chief Uche Nwosu, ya bukaci yan jam'iyyar APC, wadanda suka kafa wata kungiya mai suna Allied Forces, dake jihar Imo da kada su juya wa jam'iyyar ta APC baya.

Chief Nwosu ya kuma shawarce su dasu ba wa gwamna Rochas Okorocha, shugaban jam'iyyar APC reshen jihar Imo hakurin adawar da suke nuna wa.

DUBA WANNAN: Gobara mai karfi ta cinye wani yanki na jihar California dake kasar Amurka

A lokacin da yayi magana da manema labarai, Nwosu ya hori kungiyar da su hada kansu da gwamnan don gyara jam'iyyar kafin zuwan zaben 2019.

Ya kara da cewa "Kamar yanda yake yanzu, zabi daya gare su yan adawar, shine barin jam'iyyar su koma wata, amma a tunanin mu hakan ba dole bane. Muna bukatar da su zauna kuma suyi aiki tare da jam'iyyar saboda suna da rawar takawa gurin ganin sun karfafa jam'iyyar."

Nwosu, wanda ya nuna cigaban da ake samu a kwanakin nan a jam'iyyar ya nuna cewa babu shakka Okorocha har yanzu yana da ta cewa a jam'iyyar a matakin jiha da kuma kudu maso gabas gaba dayanta.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel