Gobara mai karfi ta cinye wani yanki na jihar California dake kasar Amurka

Gobara mai karfi ta cinye wani yanki na jihar California dake kasar Amurka

Sanadiyyar wata mummunar gobada data tashi a jihar California dake kasar Amurka, gidaje masu dumbin yawa sun kone inda ta raba mutane masu yawan gaske da gidajen su, dalilin da yasa aka dinga kwashe mutanen daga gidajen nasu

Gobara mai karfi ta cinye wani yanki na jihar California dake kasar Amurka

Gobara mai karfi ta cinye wani yanki na jihar California dake kasar Amurka

Sanadiyyar wata mummunar gobada data tashi a jihar California dake kasar Amurka, gidaje masu dumbin yawa sun kone inda ta raba mutane masu yawan gaske da gidajen su, dalilin da yasa aka dinga kwashe mutanen daga gidajen nasu.

DUBA WANNAN: Mutane 23 sunji munanan raunuka sanadiyyar hadarin mota a wani kauye dake kan hanyar Abuja

Shugaban hukumar kula da sashen kashe gobara na jihar Jonathan Cox shine ya fitar da sanarwar, inda yake cewa, a yankin Clearlake Oaks na jihar California gobarar ta kama wani dan karamin daji, sai dai gobarar ta yadu ne sanadiyyar kadawar da iska take yi, inda gobarar ta dinga karfi har na tsawon kilomita 31.

Cox yace, gwamnati ta bada umarnin kwashe mutane sama da dubu 3 daga yankin Spring Valley, inda gidaje masu yawan gaske suka kone kurmus.

Cox yace, suna yin iya bakin kokarin su domin gani dalilin tashin gobarar, sannan ya tabbatar da cewa babu wanda ya mutu ko jikkata sanadin gobarar.

Rahotanni sun nuna cewa an aika ma'aikatan kashe gobara akalla 230 tare da jirgi mai saukar ungulu da manyan motoci domin kashe gobarar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel