Ko ku fito da Nnamdi Kanu ko kudin ku su bi ruwa – Kotu ta fadawa Sanata Abaribe

Ko ku fito da Nnamdi Kanu ko kudin ku su bi ruwa – Kotu ta fadawa Sanata Abaribe

Jaridar The Tribune ta rahoto cewa Kotu ta fadawa wadanda su ka tsayawa Nnamdi Kanu a gaban shari’a da su fito da shi ko su shiga babban matsala. Sanatan na PDP yana cikin wadanda su ka bada jingina aka bada belin Nnamdi Kanu.

Ko ku fito da Nnamdi Kanu ko kudin ku su bi ruwa – Kotu ta fadawa Sanata Abaribe

Kotu ta fadawa Sanata Abaribe ya fito da Nnamdi Kanu

A bara ne dai Alkali mai shari'a Binta Nyako ta ba Jagoran na Kungiyar IPOB beli bayan ya shafe fiye da shekara daya da rabi a tsare. An saki Kanu ne bayan an tabbatar da cewa yana da larurar rashin lafiya. Sai dai kuma yanzu an rasa inda ya shige.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya gargadi Malaman Jami'an Najeriya

Yanzu dai ana kokarin cigaba da shari’a amma Hukuma ta rasa inda Nnamdi Kanu yake don haka Kotu ta nemi Eyninnaya Abaribe da wani Bayahude da wani mutum da ya tsaya masa har aka ba sa beli da su fito da shi ko kuma su Kotu ta dauki mataki.

Ogechi Ogbona wanda shi ne Lauyan da ke kare Sanatan ya nemi a cire hannun sa daga shari’ar sai dai Kotu tace ba za ayi hakan ba sai ya fito da Kanu. Yanzu dai an ma nemi sauran wadanda su ka sa hannu aka saki Nnamdi Kanu an rasa a Kotun.

Kotu ta ba Sanatan na Kudancin Abia Abaribe sharuda 3 a zaman da tayi inda ake nemi ya fito da Nnamdi Kanu ko kuma ya hakura da Naira Miliyan 100 da ya mikawa Kotu a matsayin jingina ko kuma a ba shi lokaci ya nemo sa wanda hakan ya zaba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel