Dubu ta cika: Wadansu da suka yiwa gawa fyade sannan suka gasa namanta suka cinye sun shiga hannu

Dubu ta cika: Wadansu da suka yiwa gawa fyade sannan suka gasa namanta suka cinye sun shiga hannu

- Rashin imani ya sanya wasu mutane aikata mummunan aiki da sunan tsafin kudi

- Bayan yiwa wata budurwa fyade sun kashe ta sannan suka ci namanta

- Amma jami'an 'yan sanda sun damko su har ma da sauran abokan aikin nasu

Asirin wasu mutane uku ya tonu bayan sun hada baki wajen yiwa budurwa mai shekaru 19 fyade kafin su kashe ta sannan suka sake yiwa gawarta fyade kuma suka gasa namanta suka cinye.

Wannan mummunan lamari dai ya faru ne a karamar hukumar Adavi ta jihar Kogi

An dai gurfanar da jagoran wadannan masu aika-aikar Oluwasegun Otaru da yake ikirarin shi malamin addinin kirista ne a cocin Voice of Canaan Temple C&S Aladura a babbar shelkwatar ‘yan sanda ta hijar Kogi da sauran mutane biyun masu suna Oluwasegun Samuel da Yakubu Abdulmumuni.

Dubu ta cika: Wadansu da suka yiwa gawa fyade sannan suka gasa namanta suka cinye sun shiga hannu

Dubu ta cika: Wadansu da suka yiwa gawa fyade sannan suka gasa namanta suka cinye sun shiga hannu

Wadanda ake zargin sun amsa laifinsu na aikata fyaden kafin da bayan mutuwar budurwar sannan suka gasa namanta suka ci kafin daga bisani su binne ragowarta duk wai da sunan suna aikata asirin samun kudi.

Jami’an ‘yan sanda sun samu nasarar cafke karin wasu mutane bakwai dake da alaka da wancan balahira, kuma Jagoran tawagar Otaru ya shaidawa ‘yan sandan cewa shi malamin addinin kirista ne amma maitar son kudinsa ce ta rude shi ya aikata wannan mummunan abu.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun kashe Sarki a wata jiha a kasar nan

Sannan ya tabbatarwa da ‘yan sandan cewa kafin wannan lokacin ma ya taba fiddo da gawar mutane har biyu da yayi tsafin kudin amma shiru kake ji kudin yaki samuwa.

Hakan ce ma ta sanya sa shi daukar sabon mataki na jarraba samun mutum rayayye tunda matattun sunki bayar da hadin kai.

Wannan sabon tsari ne ya fara aiki kan marigayya Mercy Moses kuma a karshe yana sa ran samun kudi har Naira N2.5m bayan kammala tsafin.

Mai magana da yawun ‘yan sanda na jihar William Aya, ya tabbatar da cewa an kama wadanda ake zargin ne bayan samun rahotan bacewar budurwar.

Ragowar mutane bakwan da aka kama sun hada da Ubile Attah, Abdul Tijani, Julius Alhassan, Onuche James, Akwu Audu, Shehu Haliru da kuma Amedu Yakubu.

Yanzu haka dai ‘yan sandan na cigaba da gudanar da bincike kuma da zarar an kammala za’a kaisu kotu, a cewar kakakin ‘yan sandan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel