An yi ba ayi ba: An zargi Gwamnatin Buhari da aikata irin laifin PDP

An yi ba ayi ba: An zargi Gwamnatin Buhari da aikata irin laifin PDP

- An zargi Gwamnatin Shugaba Buhari da keta alfarmar Bil Adama a Najeriya

- Femi Falana SAN ya zargi wannan Gwamnati da yin irin barnar da PDP tayi

- Lauyan ya bayyana yadda Jami’an DSS su ka kama wata ‘Yar jarida tun 2016

Femi Falana wanda fitaccen Lauya ne da ke kare hakkin Bayin Allah a Najeriya ya zargi Gwamnatin APC ta Shugaba Muhammadu Buhari da keta alfarma da hakkin Bil Adama kamar yadda dai aka rika yi a lokatun baya.

An yi ba ayi ba: An zargi Gwamnatin Buhari da aikata irin laifin PDP

Falana yace an rabu da bukar an haifi abu tsakanin PDP da APC

Babban Lauyan Kasar Mista Falana SAN wanda yana cikin ‘yan gaba-gaba wajen fafatukar kare hakkin al’umma yace Jam’iyyar APC tana yin irin abin da PDP tayi na saba doka da ka’idar Kasa lokacin tana mulkin Najeriya.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya bayyana masu ruwa da tsaki a rikicin Filato

Lauyan ya bayyana yadda ya rika yi wa tsohuwar Jam’iyyar Shugaba Buhari kokari a 2003 domin fito masu da hakkin su amma sai ga shi yanzu Jam’iyyar Shugaba Buhari ta samu mulki tana yin abin da ta ga dama a Kasar.

Falana SAN ya koka da yadda Jami’an tsaro na farar kaya su ke cigaba da tsare wata ‘Yar jarida tun 2016 da aka kama ta. Fadar Shugaban Kasa dai ta musanya lamarin amma har yanzu ba a maka wannan Baiwar Allah a Kotu ba.

Dama kun ji cewa a karshen makon can ne aka kai wani hari a Garin Barkin Ladi da ke Jihar Filato wanda hakan yayi sanadin mutuwar mutane akalla 86. Wannan dai ya sa Shugaba Muhammadu Buhari ya fitar da jawabi na jaje.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel