'Yan bindiga sun kashe Sarki a wata jiha a kasar nan

'Yan bindiga sun kashe Sarki a wata jiha a kasar nan

Mutanen garin Mgbee dake yankin karamar hukumar Orlu dake jihar Imo sun fada cikin tashin hankali da jimami a ranar Lahadin nan data gabata sanadiyyar kisan gillar da 'yan bindiga suka yiwa sarkin su na gargajiya, Eze Brenden Ibekwe

'Yan bindiga sun kashe Sarki a wata jiha a kasar nan

'Yan bindiga sun kashe Sarki a wata jiha a kasar nan

Mutanen garin Mgbee dake yankin karamar hukumar Orlu dake jihar Imo sun fada cikin tashin hankali da jimami a ranar Lahadin nan data gabata sanadiyyar kisan gillar da 'yan bindiga suka yiwa sarkin su na gargajiya, Eze Brenden Ibekwe.

DUBA WANNAN: Akwai yiwuwar Mikel Obi ba zai buga wasan gobe ba na Najeriya da Argentina

Majiyarmu Legit.ng ta samu labarin cewar 'yan bindigan sun ajiye gawar sarkin akan babbar hanyar Orlu zuwa Owerri, kilomita kadan daga fadar shi, sannan suka gudu da kayan shi, wadanda suka hada da carbin sa na sarauta, agogo da kuma wayar shi ta salula.

Mun samu labarin cewar, 'yan bindigan sunyi ta harbin shi har sai da yace ga garin kunan, sannan sai da suka tabbatar da cewa baya motsi, sannan suka tafi. Rahotanni sun nuna cewar mutanen kauyen sun fada cikin rikici na siyasa, dalilin da yasa mutanen kauyen fara rikici da junan su.

Jami'in hulda da jama'a na hukumar 'yan sandan jihar, Andrew Enwerem, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, yace kwamishinan 'yan sandan jihar, Dasuki Galadanchi, ya bada umarnin gabatar da bincike mai karfi akan lamarin.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel