Babu wanda zai iya daure ni saboda na kiyaye mutunci na – Shugaba buhari ya cikawa ‘yan adawa baki

Babu wanda zai iya daure ni saboda na kiyaye mutunci na – Shugaba buhari ya cikawa ‘yan adawa baki

Shugaba buhari ya bayyana cewar babu wanda zai iya daure shi bayan ya kamala wa’adin mulkin sa saboda yak are mutunci da kimar sa.

Buhari ya bayyana cewar da bai kiyaye mutuncin sa ba a mukaman day a rike a baya, da tuni ya dade a garkame a gidan yari.

Shugaban kasar na wadannan kalamai ne yayin day a karbi bakuncin mambobin majalisar koli ta Sharia a fadar gwamnatin tarayya a yau, Litinin, kamar yadda mai magana da yawun sa, Mallam Garba Shehu, ya sanar.

Babu wanda zai iya daure ni saboda na kiyaye mutunci na – Shugaba buhari ya cikawa ‘yan adawa baki

Shugaba Buhari
Source: Depositphotos

Buhari ya kara da cewar ba zai taba nadamar yin riko da gaskiya ba tare da bayyana wa mambobin majalisar koli ta sharia cewar yana farinciki yadda ya hana na kusa da shi karba ko neman kwangila.

DUBA WANNAN: Kotu ta tsayar da ranar yanke hukunci a kan karar da Dasuki ya shigar da gwamnatin tarayya

Kazalika ya shaida masu cewar ba ya bayar da kwangila kuma bai damu da waye ya samu kwangila ko waye bai samu ba.

Na rike mukamai a baya, har a ma’aikatar man fetur. Da tuni an kulle ni da na mallakawa kai na rijiyar mai amma saboda na kare mutunci na, ban yi hakan ba kuma ba na nadama har yanzu,” a kalaman shugaba Buhari.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel