Boko Haram: Shugaba Buhari ya damu da halin da ‘Yan gudun hijira su ke ciki- Garba Shehu

Boko Haram: Shugaba Buhari ya damu da halin da ‘Yan gudun hijira su ke ciki- Garba Shehu

Labari ya zo mana daga Jaridar nan ta Daily Trust cewa Mai magana da yawun bakin Shugaban Kasa watau Malam Garba Shehu yayi magana game da Bayin Allah da ke Yankin Arewa maso Gabashin Kasar ke gudun hijira a cikin Najeriya.

Boko Haram: Shugaba Buhari ya damu da halin da ‘Yan gudun hijira su ke ciki- Garba Shehu

Shugaban Kasa Buhari bai da tunanin da ta wuce na IDP inji Garba Shehu

Mai magana da yawun Shugaban Kasar ya fadi wannan ne lokacin da wasu ‘Yan gudun hijira su ka yi tattaki a babban Birnin Tarayya Abuja domin yabawa kokarin Gwamnatin Shugaban Kasa Buhari da Jami’an tsaro na maida su gidajen su.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya rushe Hukumar NABTEB

Shugaban Kasar dai ya bayyana cewa yana kokarin ganin sauran wadanda ke sansanin gudun hijira a Arewacin Kasar sun tattara sun koma gidajen su. Sama da mutane 2000 dai yanzu sun bar sansanin IDP sun koma gidajen su da su ka baro.

Malam Shehu wanda shi ne Kakakin Shugaban Kasar yace maida kowa gidan na sa bayan irin barnar da Boko Haram su kayi ba abu bane mai sauki. Shehu dai yace gudumuwar da kasashen waje ke badawa na taimakawa Yankin da abin ya shafa.

Garba Shehu ya bayyana cewa Shugaba Buhari ya damu matuka da halin da masu gudun hijira su ke ciki kuma kullum da tunanin su yake tashi. Wata Baiwar Allah da tayi magana a madadin ‘Yan gudun hijiran ta yabawa kokarin wannan Gwamnatin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel