Rashawa: Buhari ya rusa shuwagabannin wata hukumar shirya jarabawa a Najeriya

Rashawa: Buhari ya rusa shuwagabannin wata hukumar shirya jarabawa a Najeriya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da rusa shuwagabannin kwamitin gudanarwa na hukumar shirya jarabawar makarantun kimiyya da fasaha, NABTEB, ba tare da wata wata ba, inji rahoton kamfanin dillancin labaru, NAN.

Babban sakataren ma’aikatan Ilimi na kasa, Sonny Echono ne ya sanar da haka a ranar Litinin, 25 ga watan Yuni, yayin wata ganawa da yan jaridu, inda yace baya ga rusa kwamitin, Buhari ya umarci ministan Ilimi, Adam Adamu da ya tabbata ya iganta hukumar don biyan bukatun da aka kafata don su.

KU KARANTA: Wata sabuwa: Kalli wasu shanu dake kiwo a cikin majalisun dokokin Najeriya

Haka zalika, Buhari ya soke dakatarwar da kwamitin ta yi ma jami’in mulki na hukumar, Farfesa Ifeoma Abanihe da wasu daraktoci guda hudu, inda yace sallamar tasu bata yi daidai da tanadin doka ba, inda yace kwamitin ta wuce gona da iri, don kuwa hakan ba aikinta bane.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kwamitin ta sallami Daraktocin ne a ranar 19 ga watan Yuni a yayin wani taro da ta yi a garin Bini na jihar Edo, inda ta yi ikirarin kama shwagabannin hukumar da satar kudi naira miliyan 49.7.

Sauran daraktoci hudun da Buhari ya soke sallamarsu sun hada da: Nnasia Ndarake Asanga, Obinna Opara, Alhaji Jimoh Adewola Kasali, da kuma Edwin Osamo.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel