Kotu ta tsayar da ranar yanke hukunci a kan karar da Dasuki ya shigar da gwamnatin tarayya

Kotu ta tsayar da ranar yanke hukunci a kan karar da Dasuki ya shigar da gwamnatin tarayya

- Wata kotun gwamnatin tarayya ta tsayar da ranar 2 ga watan Yuli a matsayin ranar da zata yanke hukunci a karar da Dasuki ya shigar da gwamnatin tarayya

- Dasuki yam aka gwamnatin tarayya a kotu ne bisa cigaba da tsare shi ba bisa ka’ida ba

- Dasuki na neman kotu ta tilasta gwamnatin gwamnatin tarayya biyan shi diyyar kudin tsare shi, ba bisa ka’ida ba, da yawan su ya kai biliyan N5bn

Wata kotun gwamnatin tarayya ta tsayar da ranar Litinin, 2 gawatn Yuli, a matsayinranar da zata yanke hukunci a shari’ar da ake yi tsakanin tsohon mai bawa shugaban kasa shawara a kan harkokin tsaro, Sambo Dasuki, da gwamnatin tarayya.

Kotu ta tsayar da ranar yanke hukunci a kan karar da Dasuki ya shigar da gwamnatin tarayya

Sambo Dasuki

Dasuki ya maka gwamnatin tarayya a kotu ne bisa cigaba da tsare shi, tun bayan kama shi a shekarar 2015, duk da kotu tayimumarnin a sake shi. Dasuki na neman kotun ta tilasta gwamnatin tarayya biyan shi kudin diyya, biliyan N5bn, saboda take hakkin san a bil’adama.

DUBA WANNAN: ‘Gyauron ‘yan PDP ke bata mana akidar jam’iyyar APC’ – Tinubu

Lauyan dake kare Dasuki, Ahmed Raji (SAN) ya kafe kan cewar gwamnatin tarayya ba ta bi hanyoyin da suka dace ba wajen tsare Dasuki na tsawon fiye da shekaru biyu ba.

Cikin wadanda Dasuki ke kara tare da gwamnatin tarayya akwai shugaban hukumar tsaron farin kaya (DSS), Lawal Daura, da Ministan shari’a na kasa, Abubakar Malami.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel