PDP ta taya Oshiomhole murnar nasarar zama shugaban jam’iyyar APC na kasa

PDP ta taya Oshiomhole murnar nasarar zama shugaban jam’iyyar APC na kasa

Shugaban jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na kasa, Uche Secondus ya taya Kwamrad Adams Oshiomhole farin cikin kasancewa sabon shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa.

Channels TV ta ruwaito cewa Secondus a wata sanarwa das a hannun mai bashi shawara a kafofin watsa labarai, Nike Abonyi a ranar Litinin, 25 ga watan Yuni ya taya Oshiomhole murna kan wannan sabon matsayi da ya hau.

“A madadin jam’iyya ta, wato babban jam’iyyar adawa PDP ina taya ka murna sannan ina addu’an Allah yasa damokradiyya ta samu Karin martaba a yanzu da ka hau kujerar shugabancin jam’iyyar ka.

PDP ta taya Oshiomhole murnar nasarar zama shugaban am’iyyar APC na kasa

PDP ta taya Oshiomhole murnar nasarar zama shugaban am’iyyar APC na kasa

"Ina baka tabbacin cewa a shirye jam’iyyar PDP take ta yi adawa mai inganci ta yadda za’a tafiyar da dukkan hammaya kan damokradiyya." Inji shi

KU KARANTA KUMA: Wata sabuwa: Kalli wasu shanu dake kiwo a cikin majalisun dokokin Najeriya

A baya Legit.ng ta tattaro cewa Kwamishinan bayanai na jihar Kano, Kwamrad Mohammed Garba, ya caccaki tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso kan kauracewa babban taron APC da aka gudanar a Abuja a karshen mako.

A ranar Litinin, 25 ga watan Yuni, Garba ya bayyana hujjar da Kwankwaso ya bayar na kin halartan taron a matsayin karya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel