Wata sabuwa: Kalli wasu shanu dake kiwo a cikin majalisun dokokin Najeriya

Wata sabuwa: Kalli wasu shanu dake kiwo a cikin majalisun dokokin Najeriya

Wani abu ban mamaki daya faru a majalisun dokokin Najeriya dake babban birnin tarayya Abuja shi ne yadda wasu makiyaya suka afka da shanunsu cikin majalisar da nufin kiwo, inji rahoton jaridar The Cables.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wani bidiyo ya nuna shanun suna kiwo a wani bangare na majalisar ba tare da wani tsangwama ba, wanda hakan ya janyo cece kuce a shafukan yanar gizo.

KU KARANTA: Matar wani gwamnan Arewa ta biya ma wata mara lafiya naira N1,300,000 kudin asibiti

Sai dai abinda ya ja hankali game da wannan lamari shine akwai wata doka da ta hana kiwon dabbobi a cikin garin babban birnin tarayy Abuja, don gudun faruwar haddura, da kuma bata gari da kasha.

Bidiyon:

Haka zalika irin wannan dokar hana kiwo da wasu gwamnoni suka kaddamar ya haifar da rikice rikice a jihar da suka yi sanadin salwantar rayukan jama’a da dama a wadannan jihohi, daga cikinsu akwai Taraba da Benuwe.

Ko a karshen makon da ya gabata, sama da mutane Tamanin da shidda sun rasa rayukansu a sakamakon rikicin makiyaya da manoma da ya kaure a jihar Filato.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel