Akalla mutum 85 su ka mutu a harin da aka kai a Filato - 'Yan Sanda

Akalla mutum 85 su ka mutu a harin da aka kai a Filato - 'Yan Sanda

- Ana zargin wasu Makiyaya da kai wasu munanan hari a cikin Garin Filato

- Hakan yayi sanadiyyar mutane sama da 80 inji Jami’an tsaro da ke Jihar

Mun samu labari daga Jaridar Premium Times cewa hare-haren da aka kai a Garin Barkin Ladi da ke Jihar Filato a karshen makon nan yayi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 86 a tashi guda.

Akalla mutum 85 su ka mutu a harin da aka kai a Filato - 'Yan Sanda

An kashe mutane da dama a Garin Barkin Ladi jiya

A baya ani Bawan Allah da ke Garin na Barkin Ladi yayi ikirarin cewa mutanen da aka kashe sun haura 120. A Ranar Lahadi ne wasu da ake zargin cewa Makiyaya ne su ka kai wani mummunan hari a Garin na Jos inda su ka hallaka jama’a.

KU KARANTA: Rikicin Filato: Za mu yi maganin masu barna – Inji Shugaba Buhari

Harin da aka kai ne dai ya sa Gwamnatin Jihar Filato ta sa dokar-ta-baci a Yankin inda aka hana al’umma fita domin tsagaita bala’in. Jami’an ‘Yan Sanda ta bakin Tema Tyopev dai sun tabbatar da cewa an kashe mutum sama da 86.

Jami’in da ke magana da yawun bakin Rundunar ‘Yan Sandan yace an kashe mutane 86 bayan kuma gidaje sama da 50 da kuma babura kimanin 15 da aka kona. Tyopev ya kuma tabbatar da cewa yanzu haka wasu na kwance a asibiti.

A baya dai kun ji an fadi kadan daga cikin wadanda aka kashe. Rikicin dai ne ya sa Gwamna Simon Lalong ya dawo Jihar a gurguje bayan ya tafi Birnin Tarayya halartar babban gangamin Jam’iyyar APC.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel