Rikicin Filato: Abin sam babu dadi kuma za mu dauki mataki – Inji Shugaba Buhari

Rikicin Filato: Abin sam babu dadi kuma za mu dauki mataki – Inji Shugaba Buhari

- Shugaba Buhari yayi magana game da rikicin da ya barke a Garin Filato

- Gwamnati tace ba za ta kyale wadanda aka samu da laifi haka kurum ba

- Jami’an tsaro da Gwamnatin Jihar na kokarin kawo zaman lafiya a Filato

A karshen makon nan ne aka kai wani hari a Garin Barkin Ladi da ke Jihar Filato wanda hakan yayi sanadin mutuwar mutane akalla 86. Wannan dai ya sa Shugaba Muhammadu Buhari ya fitar da jawabi inda ya nuna takaicin sa.

Rikicin Filato: Abin sam babu dadi kuma za mu dauki mataki – Inji Shugaba Buhari

Shugaban kasa Buhari yayi magana kan rikicin Jos

Shugaba Muhammadu ya koka da ta’adin da aka yi a Garin Filato inda yace kisan da aka yi bai yi masa dadi ba kuma abin Allah-wadai ne. Shugaban Kasar ya kuma bayyana cewa Gwamnatin sa za tayi bakin kokarin ta na samar da tsaro.

KU KARANTA: 'Yan PDP da ke cikin mu ke dawo da mu baya - Tinubu

A shafin sadarwa na Tuwita ne Shugaban Kasar da kan sa yayi magana jim kadan bayan aukuwar rikicin a jiya Lahadi. Shugaba Buhari ya jajantawa mutanen Jihar Filato da ke tsakiyar Najeriya game da wannan ta’adi da ya auka masu.

Kamar yadda mu ka samu labari, Shugaba Buhari ya tabbatar da cewa an bayyana masa abin da ya auku. Shugaba Buhari yace Jami’an tsaro na Sojoji da ‘Yan Sanda na ba bakin kokarin su na hada kai da Gwamna Simon Lalong na kawo zaman lafiya.

Gwamnatin Buhari dai tace za ta hukunta wadanda aka samu da laifi. Rikicin da ya ci kusan mutum 100 ne dai ne ya sa Gwamna Simon Lalong ya dawo Jihar Filato a gurguje bayan ya tafi Birnin Tarayya halartar babban gangamin Jam’iyyar APC.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel