‘Gyauron ‘yan PDP ke bata mana akidar jam’iyyar APC’ – Tinubu

‘Gyauron ‘yan PDP ke bata mana akidar jam’iyyar APC’ – Tinubu

Jagoran jam’iyyar APC, Ahmed Bola Tinubu, ya bayyana cewar burbusshin ‘yan jam’iyyar PDP dake rike da mukamai a gwamnati ne ke kawo tangarda ga akidun jam’iyyar APc na son kawo canji.

Tinubu ya bayyana cewar da yawan mutanen dake rike da wasu ma’aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya, PDP c eta nada su kuma har yanzu ita suke yiwa aiki.

Jagoran na jam’iyyar APC na wadannan kalamai ne a cikin wani jawabi da ofishin sa na yada labarai ya fitar jiya, Lahadi, a Abuja.

‘Gyauron ‘yan PDP ke bata mana akidar jam’iyyar APC’ – Tinubu

Bola Tinubu

Kazalika ya zargi jam’iyyar PDP da niyyar barnata tattalin arzikin Najeriya na tsawon shekaru 60 kafin jam’iyyar APC ta kayar das u a zaben shekarar 2015.

Akwai abun day a zama dole na fada saboda muhimmancin sa; akidun jam’iyyar APC na son kawo gyara da canji a harkokin mulkin Najeriya na samun tangarda ne saboda gyauron ‘yan jam’iyyar PDP da har yanzu ke rike da mukamai masu muhimmanci a cikin gwamnatin tarayya,” in ji Tinubu.

DUBA WANNAN: Gwamna Badaru ya sanar da sakamakon kujerun da aka fafata a kan su, duba wadanda suka yi nasara da kuri'un da suka samu

Sannan ya cigaba da cewa, “har yanzu suna yiwa PDP aiki ne ta hanyar lalata duk wata manufa ta cigaban kasa da muka bijiro da ita. Ba zamu cigaba da yarda da hakan ba, dole mu kakkabe gyauron PDP daga mukaman masu muhimmanci domin mu samu sukunin kyautatawa ‘yan Najeriya.”

Saidai kalaman na Tinubu basu yiwa jam’iyyar PDP dadi ba, sannan ta bayyana cewar gwamnatin APC na son fakewa da hakan domin korar wasu mutane daga aikin su, musamman wadanda basu da ra’ayin jam’iyyar ko kuma sun ki bawa jam’iyyar dammar cvin Karen su babu babbaka.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel