Karyar karatu: Jami’an yaki da rashawa sun yi ram da shugaban kwalejin kimiyya da fasaha

Karyar karatu: Jami’an yaki da rashawa sun yi ram da shugaban kwalejin kimiyya da fasaha

Shugaban kwalejin kimiyya da fasaha na garin Igbajo na jihar Osun, Dakta Akinola Olaolu ya shiga hannun hukumar yaki da zamba da makamantan laifuka, ICPC, akan takardar karatun bogi da yayi a baya, inji rahoton jaridar The Punch.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito an kama Olaolu ne a ranar Juma’ar data gabata, sakamakon hada takardar karatun digirin digirgir na bogi, wanda yayi ikirarin wai ya samota ne daga jami’ar gwamnatin tarayya dake Ibadan.

KU KARANTA: Gardawa 4 sun Lakada ma Mijin yar uwarsu duka har lahira, sakamakon cutarta da yake yi

A watan Disamnar 2015 ne Olaolu ya fara aiki a kwalejin kimiyyar, da mukamin mataimakin shugabanta, amma dayake yayi ikirarin wai ya yi karatun digirin digirgir, sai daga bisani mahukunta suka sallami tsohon shugaban kwalejin, suka daura shi.

Karyar karatu: Jami’an yaki da rashawa sun yi ram da shugaban kwalejin kimiyya da fasaha

Olaowu

Sai dai bayan darewarsa mukamin shugaban kwalejin, Olaolu bai bayyana ma mahukunta kwaljein kwalinnasa ba, kuma da aka tuntubi jami’ar Ibadan, inda yace a can yayi karatun nasa, sai suka ce basu da masaniyar karatun nasa.

Kaakakin jami’ar yace lambar dalibta da Olaolu ya bayyana a matsayin lambarsa yayin da yake jami’ar Ibadan, hadi ne kawai, ma’ana bana gaskiya bane.

Zuwa yanzu dai mahukunta a kwalejin sun fara neman sahihin mutumin da zasu nada sabon shugaban kwalejin, kamar yadda wani babban daga cikin mahukuntar ya tabbatar, amma shugaban hukumar gudanarwa na kwalejin ya ki cewa komai game da lamarin, inda yace suna bincike ne.

Itama Kaakakin hukumar ICPC, Rasheedat Okoduwa ta tabbatar da kama Olauwo, inda tace laifin da ake zarginsa da aikatawa ya saba ma sashi na 465 na kudin hukunta manyan laifuka, tare da sashi na 25 na dokokin yaki da rashawa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel