Yanzu Yanzu: Rundunar sojin Najeriya sun kama masu kaiwa yan Boko Haram mai

Yanzu Yanzu: Rundunar sojin Najeriya sun kama masu kaiwa yan Boko Haram mai

Dakarun 301 Artillery Regiment sun kama wasu masu kaiwa yan ta’addan Boko Haram man fetur guda biyu a Nafada, jihar Gombe.

Mutanen da aka kama sune Mohammed Adamu Zika direba da kuma Bukar Adamu Haji, mataimakin manajan wani gidan mai a jihar Gombe yayinda dayan mai aiki tare da su ya ware. A yanzu haka dakarun soji sun kammala shiri don kama shi.

A yanzu haka masu laifin biyu na amsa tambayoyi inda daga bisani za’a mika su ga hukumar da ta dace domin hukunci.

Rahotanni sun tattaro cewa an hana gidajen mai dake Nafada saida man fetur mai yawa ga masu motoci.

Ga hotunansu a kasa:

Yanzu Yanzu: Rundunar sojin Najeriya sun kama masu kaiwa yan Boko Haram mai

Yanzu Yanzu: Rundunar sojin Najeriya sun kama masu kaiwa yan Boko Haram mai

Yanzu Yanzu: Rundunar sojin Najeriya sun kama masu kaiwa yan Boko Haram mai

Yanzu Yanzu: Rundunar sojin Najeriya sun kama masu kaiwa yan Boko Haram mai

KU KARANTA KUMA: In kana duniya kasha kallo: An gano wani kashin kunkuru mai shekaru miliyan 150 a duniya

A halin da ake cciki, Legit.ng ta tattaro cewa Hukumar sojin sama na Najeriya tace ta tura jiragen yaki guda bakwai zuwa jihohin Benue da Taraba a aiki da take na Operation Whirl Stroke, domin magance rikicinmakiyaya da manoma a jihohin guda biyu.

Shugaban hafsan sojin sama, Air Marshal Sadique Abubakar, ya tabbatar da tura jiragen a Makurdi, jihar Benue, yayin wani kaddamar da jiragen a ranar Asabar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel