An kama masu yunkurin kai hari kan Musulmi

An kama masu yunkurin kai hari kan Musulmi

Rundunar 'Yan sanda na kasar Faransa sun yi ram da wasu mutane 10 da ke da nasaba da kungiyoyin 'yan ta'adda masu tsatsauran ra'ayi domin wani yunkuri da suka kitsa na kai hare-hare akan Musulmi.

An yi ram da wasu daga cikin mutanen ne a wurare daban-daban a fadin kasar, yayainda aka kama wasu a tsibirin Corsica.

Hukumomin sharia'a na Faransa sun ce wadanda ake tuhuman shekarunsu na tsakanin 32 da 69 ne, sun kitsa wani mugu shiri na kai gagaruman hare-hare akan Musulmai.

An kama masu yunkurin kai hari kan Musulmi

An kama masu yunkurin kai hari kan Musulmi

Hukumar leken asiri na Faransa - DGSI - ta bayyana yadda kungiyar ta ke kokarin sayan makamai, kuma ta gano gurnati da kayan hada bama-bamai a lokacin da jami'anta suka kai wani samame a gidan da wadanda ake tuhuman su ke zama.

KU KARANTA KUMA: Oshiomhole ya bukaci wadanda suke ganin an maida su saniyar ware a APC da su cigaba da kasancewa a jam’iyyar

Sun kuma bayyana cewa kungiyar ta shirya kai hari kan wasu wurare da suka hada da masu yin zazzafan wa'azi domin ya zama ramuwar gayya ga hare-haren da masu kishin Islama suka kai a Faransa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel