Oshiomhole ya bukaci wadanda suke ganin an maida su saniyar ware a APC da su cigaba da kasancewa a jam’iyyar

Oshiomhole ya bukaci wadanda suke ganin an maida su saniyar ware a APC da su cigaba da kasancewa a jam’iyyar

A ranar Lahadi, 24 ga watan Yuni, Kwamrad Adams Oshiomhole wanda aka zaba a matsayin sabon shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ya bayyana cewa yana Allah-Allah ya fara aiki domin ya samu damar magance matsalolin jam’iyyar.

Ya bayyana hakan a ranar Lahadi a Abuja bayan kammala taron jam’iyyar na kasa inda ya zamo shugaban jam’iyyar ba tare da abokin adawa ba bayan an tabbatar da zabe.

Tsohon gwamnan na jihar Edo, da yake jawabi bayan zabar shi, ya bukaci mambobin jam’iyyar da suke ganin an maida su saniyar ware musamman yan kungiyar sabuwar PDP da su cigaba da kasancewa a jam’iyyyar wanda acewarsa suka hada hannu suka gina.

Ya ba masu fafutukar tabbacin cewa jam’iyyar karkashin jagorancin sa zata kawo hanyar da za’a shawo kan wannan lamari na magance rikicin dake cikin jam’iyyar.

Oshiomhole ya bukaci wadanda suke ganin an maida su saniyar ware a APC da su cigaba da kasancewa a jam’iyyar

Oshiomhole ya bukaci wadanda suke ganin an maida su saniyar ware a APC da su cigaba da kasancewa a jam’iyyar
Source: Depositphotos

Oshiomhole ya bayyana cewa zai tabbatar an karrama mambobin jam’iyyar da suka yi aiki domin cigabanta a dukkan matakai.

A halin da ake ciki, Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki yace lokaci zai tantance matsayinsa a jam’iyyar.

KU KARANTA KUMA: Shugaban majalisar dattawa Saraki yayi magana akan matsayinsa a APC

Shugaban majalisar dattawa tare da mambobin kungiyar sabuwar PDP sun yi korafi kan abunda suka kira a matsayin bangarenci da rashin girmamasu da jam’iyyar APC ke yi.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel