Shugaban majalisar dattawa Saraki yayi magana akan matsayinsa a APC

Shugaban majalisar dattawa Saraki yayi magana akan matsayinsa a APC

Yayinda yake maida martini kan cewa shi dan jam’iyyar APC ne, amma jam’iyyar ba tasa bace, Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki yace lokaci zai tantance matsayinsa a jam’iyyar.

Shugaban majalisar dattawa tare da mambobin kungiyar sabuwar PDP sun yi korafi kan abunda suka kira a matsayin bangarenci da rashin girmamasu da jam’iyyar APC ke yi.

Saraki yayi wannan jawabi ne a Abuja yayinda yake sharhi akan wani jawabi da shugaban jaridar Daily Trust, Kabiru Yusuf wanda ya yabe shi kan tafiya Umra da yayi, da Rasha inda yayi jawabi ga majalisar Rasha sannan kuma ya dawo gida Najeriya don ya halarci taron APC na kasa.

Shugaban majalisar dattawa Saraki yayi magana akan matsayinsa a APC

Shugaban majalisar dattawa Saraki yayi magana akan matsayinsa a APC

Yace: “Kabiru yayi wani furuci sannan kuma ya yimun sannu da zuwa a matsayin mamba na jam’iyyar inda ya kara cewa bai da tabbacin idan jam’iyyar na yi mun maraba kamar yadda ni nake yi musu.

“Ba zan yi sharhi akan wannan ba saboda zan shafe dare ina sharhi kan haka. Ba zan so na zamo a shafin farko na jarida ba amma lokaci zai tantance hakan.

KU KARANTA KUMA: An kama malamin tsubbu da wasu 2 akan kisan yar shekara 19 domin asiri

“Tuni na san wannan cewa wannan sharhi da nayi, kannun labarai na yawancin jaridu zai zama lokaci zai tantance. Don haka ba zan yi mamaki ba don na duba jaridar This Day na ga: Shugaban majalisar dattawa yace lokaci zai tantance.”

Idan bazaku manta ba a ranar Asabar da ta gabata ne jam'iyyar APC tayi taron ta na kasa inda aka zabi tsohon gwamnan jihar Edo, Adams Oshiomhole a matsayin shugaban jam'iyyar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel