Duba jerin ranakun da N-power zata fara tantance masu kananan kwali da zasu ci moriyar shirin

Duba jerin ranakun da N-power zata fara tantance masu kananan kwali da zasu ci moriyar shirin

- Shirin gwamnatin tarayya na N-Power ya fitar da wata sanarwa ta musamman ga masu kananan kwalin karatu da suka ci moriyar shirin.

- Masu gudanar da shirin sun bayyana cewar zasu fara tantance masu kananan kwalin karatu da aka fitar da sunayen su

- Ta lissafa rukunin mutanen da zata tantance

A jiya, Lahadi 24 ga watan Yuni, shirin gwamnatin tarayya na N-Power ya fitar da sanarwa dangane da ranar da masu kananan kwalin karatu da suka ga sunayen su zasu gabatar da kan su domin tantancewa.

Duba jerin ranakun da N-power zata fara tantance masu kananan kwali da zasu ci moriyar shirin

Duba jerin ranakun da N-power zata fara tantance masu kananan kwali da zasu ci moriyar shirin

N-Power ta sanar da cewar, dukkan masu kananan kwalin karatu da suka ga sunayen su za a fara tantance su a kananan hukumomin su daga yau, Litinin, 25 ga watan Yuni.

DUBA WANNAN: An kama malamin addini da laifin kisan wata karuwa domin yin tsatsiba, duba hotunan inda aka tono ta

A sanarwa da ta fitar a shafin ta na Tuwita, N-power, ta bayyana cewar, zata fara tantance matasan ne da suka zabi bangaren gine-gine (N-Power Build), kimiyya (N-Power Hardware/software) da kuma na bangaren kere-kere (N-Power Creative).

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel