Mohammed Salah ya zama dan wata kasa daban bayan kasarsa ta haihuwa Egypt

Mohammed Salah ya zama dan wata kasa daban bayan kasarsa ta haihuwa Egypt

- Tauraruwar nasara na bibiyar Muhammed Salah duk inda ya je

- Duk da cewa an fitar da su a gasar kofin duniya, Salah ya samu wata gagarumar karramawa

- Shugaban wata kasa makwabciyar Russia ne ya karrama shi yau Lahadi

Shugaban kasar Chechnya Ramzan Kadyrov ya girmama dan wasan kwallon kafar Egypt kuma mai bugawa kungiyar kwallon kafa ta Liverpool wasa da takardar zama cikakken dan kasar. Hakan ya faru ne a wani taro da aka gudanar na bankwana da kasar Russua kasancewar an cire su a gasar cin kofin duniya.

Mohammed Salah ya zama dan wata kasa daban ba Egypt

Mohammed Salah ya zama dan wata kasa daban ba Egypt

Ƙasar Masar ta zaɓi tana atisaye a ƙasar Chechenya kasancewar tan makwabtaka da kasar Russia ta daf da daf daga ɓangaren kudanci.

KU KARANTA: Wasan Najeriya, Maradona, tsohon dan ball, kuma tsohon kwach, yayo kashedi kafin wasan Najeriya

Muhammed Sallah ya shahara a Kakar wasannin da ya gabata Wanda hakan ya sanya shi cikin sahun manyan ƴan wasa na duniya.

"Kwarai da a gaske yau na sanya hannu kan takardar amincewa Mohammed Salah ya zama ɗan ƙasar Chechenya".

Kadyrov ya rubuta a shafinsa na kafar sadarwa na Telegram.

An dai baiwa Mohammed Salah wani bajo da kuma wata takarda dake tabbatar da kasancewar shi ɗan ƙasar a yayin wata liyafar cin abinci da aka shiryawa ƴan wasan kasar ta Misra.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel