Yan sanda sun cika hannunsu da wasu masu aika miyagun laifuka a jihar Legas

Yan sanda sun cika hannunsu da wasu masu aika miyagun laifuka a jihar Legas

- Dubun wasu daga cikin 'yan kungiyar asirin da suka yi mummunan fada ya fara tonuwa

- Har ma yanzu haka 21 toni sun shiga hannun 'yan sanda

Jami’an ‘yan sanda a jihar Legas sun daka wawa bayan da wadansu da ake kyautata zaton ‘yan kungiyar asiri ne suka yi wani mummunan fada a junansu wanda yayi sanadiyyar mutuwar wani mutum a yankin Alapere-Ketu.

Yan sanda sun cika hannunsu da wasu masu aika miyagun laifuka a jihar Legas

Yan sanda sun cika hannunsu da wasu masu aika miyagun laifuka a jihar Legas

Kakakin rundunar 'yan sanda na jihar ta Legas CSP Chike Oti ne ya tabbatar da faruwar haka ga manema labarai a yau Lahadi.

Inda ya ce yanzu haka wadanda ake zargin suna tsare kuma ana yi musu tambayoyi domin tatsar muhimman bayanai. Kuma duk wadanda suke da hannu a kisan tabbas za’a gurfanar da su gaban alkali domin fuskantar hukunci. Oti ya jaddada.

KU KARANTA: Da dumin sa: Dakarun soji sun yi nasarar gungun wasu ‘yan ta’adda a jihar Benuwe

A ranar 16 ga watan nan da muke ciki ne (Yuni) kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito yadda rikicin ‘yan kungiyar asirin ya janyo mutuwar wani mutum guda.

Wani mazaunin yankin da abin y faru da ya bukaci aboye sunansa ya shaidawa NAN cewa rikicin na ‘yan kungiyar asirin a yankin ya jima ana yinsa tsawon lokaci. Kuma ya bayyana sunayen kungiyoyin asirin da Eiye da Aye confraternities.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel