Mutane 880 ne muke kamawa a kullum da suke karya dokokin titi – LASTMA

Mutane 880 ne muke kamawa a kullum da suke karya dokokin titi – LASTMA

- Karya dokokin titi na cigaba da zama ruwan dare gama duniya

- Jihar Legas ta bayyana yawan mutanen da take kamawa da suka karya dokokin hanya a duk wata

Hukumar kiyaye haddura da cunkoson ababen hawa ta jihar Legas (LASTMA) ta bayyana cewa tana kama sama da mutane 880 da suke karya dokokin hanya daban-daban.

Mutane 880 ne muke kamawa a kullum da suke karya dokokin titi – LASTMA
Mutane 880 ne muke kamawa a kullum da suke karya dokokin titi – LASTMA

Shugaban hukumar Chris Olakpe ne ya bayyana hakan ga kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) a jihar Legas.

Ya ce hukumar na da ofisoshi 44 a fadin jihar wanda a kulluma suke kama masu ababen hawa sama da 20 bisa karya dokokin hanya.

Sannan ya kara da cewa da zarar an kama mai abin hawa akwai kotun tafi da gidanka da take auna laifinsa da kuma irin tarar da za’ai masa, kuma hukumar ta samar da ka’idojin kama wadanda suka aikata laifin don gujewa samun matsala.

KU KARANTA: Yan sanda sun cika hannunsu da wasu masu aika miyagun laifuka a jihar Legas

“Babu wani dan Najeriya da zaka kama ba tare da ya nemi ya turje ba, musamman masu ababen hawa na haya a jihar Legas, wanda wannan babban kalubale ne a gare mu”.

“Da ka daga hannu don tsayar da su sai ka ga sun maka giyar baya kuma hakan sai ya sanya su bugawa wanda yake bayansu”.

Amma da aka tambaye shi kan maganar kamen son kai da hukumar take, shugaban hukumar Olakpe ya ce suna binciken wannan zargin kuma duk wanda aka kama za’a hukunta.

Sanna shugaban LASTMA yayi gargadi ga jami’an hukumar da su daina tsalle suna hawa abin hawan wanda suke kokarin kamawa, domin duk wanda aka kama da yin hakan zai fuskanci hukunci.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel