Watsi da zabubbukanmu da shugabancin Oyegun tayi ya hana ni halartan taron gangamin APC - Kwankwaso

Watsi da zabubbukanmu da shugabancin Oyegun tayi ya hana ni halartan taron gangamin APC - Kwankwaso

Sanata mai wakiltan mazabar Kano ta tsakiya kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana dalilin da ya hanashi da mabiyansa halartan taron gangamin jam’iyyar APC a jiya Asabar da yau Lahadi wanda ake kan gudanarwa a yanzu a birnin tarayya Abuja.

Sanata Kwankwaso wanda ke shirin takarar kujeran shugaban kasa ya bayyana hakan ne a wani sabon jawabi da ya saki a yau Lahadi, 24 ga watan Yuni 2018 inda yace:

“Kungiyar jam’iyyar All Progressive Congress (APC) a Kano wacce nike jagoranta na mika sakon taya murnarta ga sabon shugaban jam’iyya, Comrade Adams Oshiomhole da sauran mambobin shugabancinsa.

Ina son sanar da shugabancin jam’iyyar da al’umma cewa mun yi niyyar halartan wannan taron gangami amma hakan bai yiwu ba saboda shugabancin jam’iyyar ta yi watsi dukkan zabubbukan da muka gudanar a kananan hukumomi da jiha.

Saboda haka, na yi tunanin gabatar da kanmu a irin wannan taro mai muhimmanci ba zai yi kyau ba ko da an bari mun samu daman shiga farfajiyar.

Dalili shine akwai yiwuwan cewa halartanmu zai kawo rikici kamar yadda ya faru da yan jihar Imo da Delta a jiya ko kuma fiye da haka. Saboda haka mua taya sabbin shugabanni murna.”

Banda Sanata Rabiu Kwankwaso, akwai manyan jiga-jigan jam’iyyar APC da basu halarci taron ba bisa ga rikici da ke cikin jam’iyyar tun zaben shugabannin jihohi da suka gabatar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel