Sojin saman Najeriya sunyi luguden wuta akan 'yan bindiga a jihar Benue

Sojin saman Najeriya sunyi luguden wuta akan 'yan bindiga a jihar Benue

Wani sabon farmaki ta sararin samaniya da sojojin Najeriya suka kai a wasu garuruwan da ake kyautata zaton maboyar 'yan bindiga ne yayi sanadiyyar mutuwar daya daga cikin su mai suna Terwase Akwaza.

Kamar dai yadda muka samu daga majiyar mu, sojin Najeriya din sun fara kai farmakin ne a ranar Juma'ar da ta gabata a wani kauye mai suna Ayaka dake a cikin karamar hukumar Katsina Ala.

Sojin saman Najeriya sunyi luguden wuta akan 'yan bindiga a jihar Benue

Sojin saman Najeriya sunyi luguden wuta akan 'yan bindiga a jihar Benue

KU KARANTA: Dalibai mata a BUK sun fallasa yadda malaman su ke lalata da su

Legit.ng ta samu haka zalika daga bakin mai ba gwamnan jihar shawara kan harkokin tsaro Kanal Paul Hemba mai ritaya cewa jami'an tsaron sun samu nasarar kama wasu sauran gaggan 'yan bindigar da suka yi kokarin rugawa.

A wani labarin kuma, Daya daga cikin jiga-jigan tafiyar jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya kuma tsohon gwamnan Legas Asiwaju Bola Tinubu ya zargi jam'iyyar adawa ta PDP da shirya makarkashiyar takaita Najeriya har na tsawon shekaru 60.

Sai dai Cif Tinubu ya bayyyana cewa Allah cikin ikon sa ne ya ceto Najeriyar daga hannun su ta hanyar jam'iyyar su mai kudurin ceto kasar ta APC.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel