Jerin Jiga-jigan APC da ba a gani wajen gangamin Jam’iyyar ba

Jerin Jiga-jigan APC da ba a gani wajen gangamin Jam’iyyar ba

- Wasu tsofaffin Gwamnonin APC sun kauracewa gangamin Jam’iyyar

- Murtala Nyako da Rabiu Kwankwaso ba su sa kafa wajen taron APC ba

- Ko kurar Shugaban nPDP Kawu Baraje ba a gani wajen gangamin ba

Labari ya kai gare mu cewa wasu manyan ‘Yan Jam’iyyar APC musamman tsofaffin ‘Yan PDP ba su taka kafar su zuwa wajen babban taron APC na kasa da aka yi jiya a Birnin Tarayya Abuja ba.

Jerin Jiga-jigan APC da ba a gani wajen gangamin Jam’iyyar ba

Shugaban Kasa da Mataimakin sa da tsohon Shugaban APC a zaune

Jaridar Premium Times tace kusan duk manyan ‘Yan nPDP ba su leka wajen taron da aka yi inda ake zaben shugabannin Jam’iyya na kasa ba. Rahotanni sun nuna cewa Shugaban Kungiyar nPDP Alhaji Abubakar Kawu Baraje bai halarci taron ba.

Haka kuma dai tsofaffin Gwamnonin APC na Jihohi irin su Murtala Nyako na Jihar Adamawa ba su leko wajen wannan muhimmin taro ba. Hakan dai bai rasa nasaba da kukan da ‘Yan nPDP ke yi na maida su saniyar ware a cikin Jam'iyyar APC mai mulki.

KU KARANTA: Oyegun yayi jawabin da ya ratsa zuciyar 'Yan APC

Dama kun ji cewa tsohon Gwamna kuma Sanata na Kano watau Rabiu Musa Kwankwaso yayi watsi da babban taron Jam’iyyar da aka yi jiya Asabar inda ya tattara ya wuce gidan tsohon Mataimakin Shugaban KasaAlhaji Atiku Abubakar su ka gana.

Kusan dai Shugabannin Majalisa Bukola Saraki da Yakubu Dogara ne kurum aka gani cikin manyan ‘Yan nPDP a wajen wannan taro. Masu sharhi dai sun ce an rika hangen Saraki yana yi wa Shugaban Kasa Buhari kallon hadarin kaji a wajen gangamin.

Kun ji cewa a jiya ne Kwamared Adams Oshiomhole ne ya zama sabon shugaban Jam’iyyar APC mai mulki. Yanzu haka dai yau ake cigaba da zaben shugabannin Jam'iyyar na kasa a Birnin Abuja.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel