Zargin mallakar makamai da kuma taimakon ‘yan kungiyar neman ‘yancin Biafra ne yasa aka kama Sanata Abaribe – Lauyansa

Zargin mallakar makamai da kuma taimakon ‘yan kungiyar neman ‘yancin Biafra ne yasa aka kama Sanata Abaribe – Lauyansa

- Yayin binciken sunyi awan gaba da wasu kaya har guda 27

- Binciken dai an shafe kusan a wanni bakwai ana yinsa

- Jibi ne kuma sanatan zai bayyana a gaban kotu bisa guduwar wanda ya tsayawa kotu ta bayar beli

Lauyan Sanata Enyinnaya Abaribe ya bayyana cewa Jami’an tsaro na DSS sun tsare sanatan ne kan zarginsa da hannu cikin harkyallar makamai da kuma bayar da taimako ga ‘yan kungiyar fafutikar samun ‘yancin kasar Biafra (IPOB).

Zargin mallakar makamai da kuma taimakon ‘yan kungiyar neman ‘yancin Biafra ne yasa aka kama Sanata Abaribe – Lauyansa

Zargin mallakar makamai da kuma taimakon ‘yan kungiyar neman ‘yancin Biafra ne yasa aka kama Sanata Abaribe – Lauyansa

Lauyan sanatan mai suna Chukwuma-Machukwu Ume (SAN) ya bayyana hakan ne jiya Abuja, ya ce bisa takardar izinin da ya gani ta bincikar gidan sanatan daga kotu a ranar Alhamis, ta mayar da hankali ne akan suna neman makamai da harsasai da kuma wasu kayan laifuka.

Binciken dai an fara shi jim kadan bayan kama sanatan a Otal din Transcorp dake Abuja inda yaje domin yin aski. Kuma sun fara caje ko’ina a gidan tun karfe 5pm na yamma har zuwa 11:15pm na daren Juma’a.

KU KARANTA: Sama da jam’iyyu 100 ne zasu tsaida ‘yan takara - INEC

Sannan kuma yayin binciken sun tafi da kayayyaki har guda 27 amma duk ciki babu bindiga ko harsashi, sai dai ciki har da wayoyin hannu biyu na wasu ‘yan kasar Amurka da aka samu a gidan.

“Guda daga cikin kwamfutocin da suka dauka ta kunshi tambayoyin jarrabawar da za’a gudanar gobe Litinin 25 ga watan Yuni 2018, kuma duk rokon da mu kayi don ganin sun bamu mu kwafa sun ki amincewa”.

Zargin mallakar makamai da kuma taimakon ‘yan kungiyar neman ‘yancin Biafra ne yasa aka kama Sanata Abaribe – Lauyansa

Zargin mallakar makamai da kuma taimakon ‘yan kungiyar neman ‘yancin Biafra ne yasa aka kama Sanata Abaribe – Lauyansa

Ume ya bayyana fargabarsa kan yadda ko a watan Oktobar shekarar da ta gabata aka garkame gidan sanatan daf zai gurfana a kotu kan shari’ar shugaban IPOB Nnamdi Kanu.

“A ranar Talata 26 ga watan Yuni ne dai sanata Abaribe wanda ya tsaya aka bayarda belin Nnamadi Kanu, amma sai ga shi ranar 22 ga watan Yuni an kama shi kuma aka cigaba da tsare sa”. Inji lauyan nasa Ume.

Shi dai sanata Enyinnaya Harcourt Abaribe yayi kaurin suna wajen caccakar gwamantin shugaba Buhari, wanda koda a baya-bayan nan sai da ya zargi cusa makudan kudin da ya kai N30b ga ma’aikatar wutar lantarki a cikin kasafi kudin 2018.

Hakan ce ma ta sanya lauyansa nasa fadin wannan kamu da kai masa na da nasaba da irin caccakar da yake yiwa gwamnatin APC.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel