‘Yan nPDP sun fasa ficewa daga APC bayan manyan Jam’iyya sun sa baki

‘Yan nPDP sun fasa ficewa daga APC bayan manyan Jam’iyya sun sa baki

Mun samu labari a jiya daga Jaridar The Nation cewa tsofaffin ’Yan Jam’iyyar PDP da su ka narke cikin Jam'iyyar APC kafin zaben 2015 sun dauki mataki game da matsayar su a Jam’iyyar mai mulki a halin yanzu.

‘Yan nPDP sun fasa ficewa daga APC bayan manyan Jam’iyya sun sa baki

Shugaban ‘Yan nPDP Kawu Baraje da Shugaban Kasa Buhari

A baya tsofaffin ‘Yan PDP wadanda ake kira da nPDP sun ta kukan cewa an maida su saniyar ware a Jam’iyyar APC inda har ta kai su na barazanar sauya sheka. Yanzu dai sun zauna da manya a Jam’iyyar kuma da alamu an shawo kan su.

Yanzu dai ‘Yan nPDP sun daina maganar barin APC bayan da wasu Gwamnoni da kuma Jiga-jigan Jam’iyyar su ka zauna da su a Ranar Juma’a. An tabbatarwa tsofaffin ‘Yan PDP cewa za a duba duk koke-koken su kuma a dauki mataki.

KU KARANTA: Kwankwaso yayi watsi da babban taron APC ya sulale yayi kus-kus da Atiku

An dai yi wannan zaman ne da ‘Yan nPDP lokacin da ake shiryawa gangamin APC na kasa wanda aka yi a jiya. Wani daga cikin manyan ‘Yan Jam’iyyar APC da ya nemi a boye sunan sa yace ya zama dole a nemi sulhu a Jam’iyyar mai mulki.

Bayan zaman da aka yi da wasu manyan na APC ne da su Kawu Baraje sai aka shirya ‘Yan nPDP din su ka gana da wasu manyan Gwamnonin Jihohi. APC kokarin sasanta kan ‘Ya ‘yan na ta ne ganin cewa an fara hangen zabe mai zuwa na 2019.

‘Yan nPDP sun koka da yadda Shugaban Kasa Buhari yayi watsi da korafin na su inda su kace kuma Jam’iyya ba tayi bakin-kokarin ta na ganin an yi sulhu ba. Wata Majiya daga nPDP ta nuna cewa zai yi wahala su bar APC su koma wata Jam’iyyar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel