Ba mu da alhakin Mutuwar Jami'in dan sanda a Jihar Kaduna - Kungiyar Shi'a

Ba mu da alhakin Mutuwar Jami'in dan sanda a Jihar Kaduna - Kungiyar Shi'a

Kungiyar Shi'a ta Najeriya ta barrantar da kanta daga alhakin kisan jami'in dan sanda da ya afku cikin jihar Kaduna a ranar Alhamis din da ta gabata.

A yayin ci gaba da gudanar da shari'ar jagoran kungiyar, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, mambobin kungiyar sun yi gangami wajen gudanar da zanga-zanga a farfajiyar Kotun ta jihar Kaduna.

Legit.ng ta fahimci cewa, a yayin wannan kai da kawowa tsakanin mambobin kungiyar da jami'an tsaro na 'yan sanda, wani jami'i guda ya rasa ransa da ake zargin 'yan kungiyar ke da alhakin mutuwar sa.

Kungiyar cikin wata sanarwa yayin ganawa da manema labarai cikin jihar ta Kaduna a ranar Asabar ta yau ta bayyana cewa, babu gaskiya cikin zargin da ake a kan mambobin ta yayin gudanar da zanga-zanga ta nuna rashin goyon bayan ci gaba da tsare shugabanta, Sheikh Zakzaky.

Ba mu da alhakin Mutuwar Jami'in dan sanda a Jihar Kaduna - Kungiyar Shi'a

Ba mu da alhakin Mutuwar Jami'in dan sanda a Jihar Kaduna - Kungiyar Shi'a

A yayin ci gaba da ganawa da manema labarai, wani Sakataren ta Abdulmumin Giwa ya bayyana cewa, tun kafuwar wannan kungiya cikin kasar Najeriya karkashin jagorancin shugaban ta ba ta taba yunkurin janyo tashin-tashina da fitina a kasar nan ba duk da irin cin kashin da ake yiwa mambobin ta a fadin kasar nan.

A kalaman sa, "mu na da cikakkiyyar shaida da take bayyana yadda babban jami'in dan sanda ya yi gamo da wasu 'yan baranda da ake kira 'yan rundunar sa kai kwana guda kafin mutuwar sa a unguwar Kinkinau, inda suka kulla tuggun kawar da shi daga doron kasa a yayin fitowar mambobi mu domin gudanar da zanga-zangar lumana."

"Hakan ya faru ne domin a shafa mana bakin fenti da bata sunan mu a idanun al'ummar kasar na da za su juya baya a gare mu.Wannan rahoton kisan babban jami'in ya watsu ne ta hanyar tuggu da kisisinar wasu mutane da suka nufaci yi mana cune da bata mana suna. Wannan sakamakon wani aiki ne na haɗin gwiwar 'yan sanda da kuma 'yan baranda."

"Bugu da kari, mu saurari kakakin 'yan sanda na jihar rana guda kafin afkuwar wannan lamari inda yake ikirarin cewa akwai yaki gobe kuma shi karan kansa zai fito da ta sa bindigar kirar AK47."

DUBA WANNAN: Ba za mu rangwantawa Kasar Argentina ba - Ahmad Musa

"Hakazalika mun saurari wani jami'in dan sanda yana shaidawa abokan sa dake rayuwa a yankunan Babbar Kasuwa ta Tudun Wada cewa, su kauracewa wannan yanki shine mafi a'ala a gare su domin kuwa za a gudanar da wani aiki na musamman a gobe saboda haka su san inda dare ya yi ma su."

"Wasu rahotanni da muka samu sun bayyana cewa, hukumar 'yan sanda sun kulla wani makirci tare da 'yan baramda da ake kira 'yan rundunar sa kai akan za su bi gida-gida wajen kai hari kan mambobin kungiyar mu ta Shi'a dake jihar Kaduna."

A yayin haka kuma jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, tsohon gwamnan jihar Edo Adams Oshiomhole, shine ya lashe zaben kujerar shugaban jam'iyyar APC da aka gudanar a gangamin ta na yau a babban birnin kasar nan na Abuja.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel