Makiyaya sun salwantar da Rayukan Mutane 18 a wani Kauyen Jihar Adamawa

Makiyaya sun salwantar da Rayukan Mutane 18 a wani Kauyen Jihar Adamawa

Kamar yadda kafar watsa labarai ta Channels TV ta ruwaito mun samu rahoton cewa, akalla rayuka 18 ne suka salwanta tare da jikkatar da dama a sanadiyar wani harin da ya afku a kayuen Dowayan dake karamar hukumar Demsa ta jihar Adamawa.

Makwabta wannan yanki da suka ziyarci kauyen sun shadaiwa manema labarai a ranar Asabar ta yau da cewa, ana zargin Makiyaya da kai wannan hari a daren ranar Juma'ar da ta gabata.

Makiyaya sun salwantar da Rayukan Mutane 18 a wani Kauyen Jihar Adamawa

Makiyaya sun salwantar da Rayukan Mutane 18 a wani Kauyen Jihar Adamawa

Mazauna kauyen na Dowayan sun bayyana cewa, makiyayan sun gudanar da wannan harin ne da misalin karfe 8.00 na daren ranar Juma'ar da ta gabata inda suka kone gidaje da dama da kuma dukiyar al'umma.

KARANTA KUMA: Hukumar 'Yan sanda ta kori jami'ai 19, ta rage mukaman 9 a jihar Ogun

Legit.ng ta fahimci cewa, a baya Makiyaya sun kai hari kan kananan hukumomin Numan, Demsa da Gerei dake jihar ta Adamawa.

Sai dai a yayin tuntubar Kakakin hukumar 'yan sanda na jihar, Othman Abubakar ya bayyana cewa, har yanzu bai samu wani rahoton dangane da wannan hari ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel