'Yan Majalisar mu ba su cancanci mu sake zaben su ba - Shugabannin Neja Delta

'Yan Majalisar mu ba su cancanci mu sake zaben su ba - Shugabannin Neja Delta

A ranar Juma'ar da ta gabata ne shugabannin yankin Neja Delta, suka kirayi al'ummar su akan su tunbuke 'yan majalisa dake wakilar su a Majalisar Dokoki ta Tarayya a zaben kasa na 2019.

Shugabannin na Neja Delta sun bayyana 'yan Majalisar yankin su dake Majalisar Tarayya a matsayin marasa jin kai da tausayin al'ummar da ba bu abinda suka kudirta sai biyan bukata na soyuwar zukatan su kadai.

Sun yi mamakin abinda wakilansu ke zaman aiwatar wa cikin Majalisar musamman Sanata Ben Bruce mai wakilcin jihar Bayelsa ta Gabas da suka yaba da hankalin sa dangane da yadda suka zuba idanu aka rushe duk wasu ababe da suka shafin yankin Neja Delta cikin kasafin kuɗin 2018.

Majalisar Dokoki ta Tarayya

Majalisar Dokoki ta Tarayya

Daya daga cikin shugabannin kuma tsohon shugaban kungiyar matasan kabilar Ijaw, Udengs Eradiri ya bayyana cewa, hankali ya gaza fahimtar yadda aka rage wasu muhimman ayyuka na yankin Neja Delta cikin kasafin kudin duk da cewa yankin ke samar da albarkatu na kudaden kasafin gaba daya.

KARANTA KUMA: Sufeto Janar ya yunkura domin kawo karshen Jinkiri cikin Albashin 'Yan sanda

Eradiri yake cewa, akwai bakin ciki da bacin rai dangane da rawar da 'yan Majalisar ke takawa inda yace su kasance da alhakin duk wata matsala a yankin Neja Delta.

Ya kara da cewa, babu shakka gwamnatin tarayya da kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari suka fi kyautatawa yankunan Kudu maso Kudu da kuma Kudu maso Gabashin kasar nan.

A yayin haka kuma jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, hukumar 'yan sanda ta Najeriya reshen jihar Ogun, ta kori jami'an ta 19 tare da zabge mukaman wasu 11 a tsakanin watan Yulin 2016 zuwa watan Yunin shekarar nan ta 2018.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel