An tabbatar da Adams Oshimole a matsayin sabon shugaban APC na kasa

An tabbatar da Adams Oshimole a matsayin sabon shugaban APC na kasa

Jam'iyyar APC ta tabbatar da tsohon shugaban kungiyar kwadoga na kasa, Kwamared Adams Oshiomole a matsayin sabon zababen shugaban ta na kasa.

Mr Oshiomole ya yi nasarar zama sabon shugaban jam'iyyar ne cikin sauki saboda dukkan sauran abokan takararsa sun janye.

Sanarwan ta fito ne daga babban taron da APC ke yi a dandalin Eagles Sqaure da ke birnin Tarayya Abuja don zaben sabbin shugabani.

An tabbatar da Adams Oshimole a matsayin sabon shugaban APC na kasa

An tabbatar da Adams Oshimole a matsayin sabon shugaban APC na kasa

DUBA WANNAN: Dalilai 5 da suka sa Buhari ya dauko Oshiomole don aiki a APC

An kuma tabbatar da zaben mataimakin shugaban jam'iyyar ta APC daga yankuna shida na kasar.

Tuni dai yan siyasa da daleget sun fara tururuwa zuwa cikin sakatariyar jam'iyyar tun a jiya Juma'a inda yan kasuwa ke sayar da kayayakin masarufi kama huluna da riguna da sauransu.

Wa'addin tsohon shugaban jam'iyyar John Odigie Oyegun da sauran shugabanin majalisar zai kare a ranar 25 ga watan Yunin 2018.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel