Sabuwar nasara kan Boko Haram, Sojin Najeriya na kara kutsawa tsakanin abokan gaba

Sabuwar nasara kan Boko Haram, Sojin Najeriya na kara kutsawa tsakanin abokan gaba

A jiya Juma'a ne hukumar Sojin Najeriya ta ce jami'anta sunyi nasarar halaka 'yan kungiyar Boko Haram guda bakwai tare da kwato wasu muggan makamai a wata hari da suka kai a kauyan Azara Kalmari da ke karamar hukumar Mafa a Jihar Borno.

Mataikamin direktan yada labarai na rundunar Operation Lafiya Dole, Kwanel Onyema Nwachukwu ne ya bayar da sanarwar a garin Maiduguri.

Nwachukwu ya ce dakarun sojin sunyi gamo da yan ta'adan ne misalin karfe 12 na rana yayin da suke gudanar da sintiri a wasu kauyukan da ke kusa da garin Marafa.

Sabuwar nasara kan Boko Haram, Sojin Najeriya na kara kutsawa tsakanin abokan gaba

Sabuwar nasara kan Boko Haram, Sojin Najeriya na kara kutsawa tsakanin abokan gaba

DUBA WANNAN: Ba a taba munafikin shugaban kasa a Najeriya kamar Obasanjo ba - Soyinka

Sanarwan ta ce sojojin sunyi musayar wuta inda suka ci galaba a kan yan ta'adan har suka kashe guda bakwai. Sojin kuma sun kwato bindigogi kirar AK 47 guda biyu da AK 56 guda daya sai kuma carbin alburusai guda 7 na musamman.

Sabuwar nasara kan Boko Haram, Sojin Najeriya na kara kutsawa tsakanin abokan gaba

Sabuwar nasara kan Boko Haram, Sojin Najeriya na kara kutsawa tsakanin abokan gaba

Dakarun sojin kuma sun kai ziyarci kauyukan Moduhum da Njimtulur da Hayaba Gana da Hashime da Azaya kura duk a kusa da garin Mafa.

Bayan sun gama da yan ta'adan da suka hadu dasu da farko, sojin sun kuma karasa zuwa kauyukan Koshebe Kanuri, Buramburi Gana, Kashakasha, Ngudda, Kezamari, Kellori, Koshiri da Ngwon duk a iyakar karamar hukumar Mafa

Nwachukwu ya ce sojin baza suyi kasa a gwiwa ba wajen cigaba da binciko wuraren da sauran yan kungiyar Boko Haram ke buya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel