Dalilai 5 da suka sa Buhari ya dauko Oshiomole don aiki a APC

Dalilai 5 da suka sa Buhari ya dauko Oshiomole don aiki a APC

Ana sauran kwana daya tak kafin gangamin taron APC ne Adams Oshiomole ya zama dan takara daya tilo na kujerar shugabancin jam'iyyar na kasa.

Abokan hammayarsa duk sun janye daya bayan daya inda Cif Ibrahim Emokpaire ne ya fara janyewa sai Farfesa Oserheimen Osunbor, daga karshe shima Clement Ebri ya janye.

Tun farko dama shugaba Muhammadu Buhari ya bawa Oshiomole goyon bayan sa hakan yasa sauran gwamnoni da jiga-jigan jam'iyyar suka mara masa baya suma.

DUBA WANNAN: Ba a taba munafikin shugaban kasa a Najeriya kamar Obasanjo ba - Soyinka

Abin tambaya a nan shine ya a kayi tsohon shugaban kungiyar kwadagon ya samu amincewar Shugaba Buhari? Legit.ng ta waiwayi dangantakar Oshiomole da Buhari tun shekarun baya don lalubo amsar tambayar.

Dalilai 5 da suka sa Buhari ya dauko Oshiomole don aiki a APC

Dalilai 5 da suka sa Buhari ya dauko Oshiomole don aiki a APC

1. Dogewar da Oshiomole ya yi na kin komawa PDP: Bayan hawan sa mulki, anyi ta yi masa matsin lamba kan ya koma PDP saboda jihar Edo ce kadai a yankin kudu-maso-kudu da APC ke mulki amma gogan naka bai koma ba.

Har yanzu ma Jihar Edo ce kadai a yankin kudu maso kudin da APC ke mulki, kuma tun kafin Buhari ya hau mulki, ya lura da irin gwagwarmayar da Oshiomole ya sha a hannun manyan yan siyasar yankin kamar Cif Tony Anenih.

2. Buhari ya gamsu da yadda Oshiomole ya magance iyayen gidan siyasa a Jihar Edo: Shugaba Buhari ya gamsu da yadda Oshiomole ya magance Cif Tony Anenih da Esama na Benin, Cif Gabriel Igbinedion wanda sune iyayen gidan siyasa a Jihar.

Dogewar Oshiomole wadda ta janyo masa bakin jini wajen gwamnatin PDP na daga cikin abubuwan da ya sanya Buhari ya janyo shi a jiki.

3. Gudunmawar da Oshiomole ya bawa Buhari a zaben 2015: Shugaba Buhari ya jinjinawa Adams Oshiomole bisa yadda ya jajirce wajen ganin APC ta samu kuri'u a jiharsa duk da cewa Buhari yana karawa ne da dan takara daga yankin na kudu maso kudu wato Goodluck Jonathan.

Jajircewar Oshiomole ne ta sa APC ta samu 46% na kuri'ar jihar wanda hakan shine mafi girma ya yankin, hakan ma yasa Buhari ya yiwa Oshiomole lakabi da 'zaki'.

Shugaban kasar kuma ya yi murnar yadda Oshiomole ya tabbatar da cewa jam'iyyar APC ne ta cigaba da mulkin jihar bayan ya kammala wa'adinsa inda gwamna Godwin Obaseki ya gaje shi.

4. Ayyukan da Oshiomole ya yi a matsayinsa na gwamna: Shugaba Muhammadu Buhari ya gamsu da irin ayyukan more rayuwa da Oshiomole ya yi a Edo duk da cewa ya kwashe lokaci mai tsawo yana fama da yan adawa na jam'iyyar PDP.

Buhari ya yabawa Oshiomole sosai lokacin da ya kawo ziyarar aiki a jihar a ranar 7 ga watan Nuwamban 2016 yayin da yake kaddamar da wasu ayyuka da Oshiomole ya yi.

Vanguard ta ruwaito cewa Buhari ya ce zai bawa Oshiomole wata mukami a kasa bayan ya kammala mulkinsa a matsayin gwamna a Edo.

Legit.ng ta tattaro cewa Buhari ya ce Najeriya za tayi rashi muddin ba ta amfana da baiwa da basira da kuzari da Oshiomole ke dashi ba.

5. Shugaba Buhari yana sha'awar irin rayuwar gwagwarmaya da Oshiomole ya yi: Vanguard ta ruwaito cewa a 2016 kafin Oshiomole ya sauka daga kujerar gwamna ya taba zuwa wata liyafar cin abinci a fadar shugaban kasa sanya da 'suit'.

An ruwaito cewa Buhari ya yi masa ba'a inda ya tambaya shi cewa "wanene wannan mutumin kuma? " cikin mamaki, Oshimole ya amsa da cewa shine. A lokacin ne Buhari ya fada masa cewa bai san shi da sa kayan ado irin suit ba, ya fi saninsa da khakinsa ta dan gwagwarmya.

Buharin ya shawarce shi kada ya yi watsi da khakin nasa da magoya bayansa suka sanshi da ita.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel