Kashe-kashen Zamfara: Masu rike ga mukaman gwamnati na cigaba da musayar kalamai tsakaninsu

Kashe-kashen Zamfara: Masu rike ga mukaman gwamnati na cigaba da musayar kalamai tsakaninsu

Manyan ma'aikatan gwamnati sun cigaba da nuna wa juna yatsa kan wanda alhakin kashe-kashen mutane da barnar dukiya da ake yi a Jihar Zamfara ya rataya a kansa inda Sanata Kabir Marafa ya ce laifin gwamnan Jihar ne.

Kabiru Marafa ya ce gwamnatin tarayya ma ta tabbatar da cewa gwamna Abdulaziz Yari ne ya gaza wajen kawo karshen kashe-kashen da 'yan bindiga ke yi a Jiharsa.

Daruruwan mutane ne suka rasa rayyukansu sakamakon hare-haren da 'yan bindiga ke kaiwa kauyuka a Jihar ta Zamfara.

DUBA WANNAN: Ba a taba munafikin shugaban kasa a Najeriya kamar Obasanjo ba - Soyinka

Mr Marafa ya ce ya dade yana kira ga gwamnan jihar ya dauki mataki a kan kashe-kashen da akeyi a Jihar amma sai ya dauke shi a matsayin makiyinsa maimakon da dauki shawarar da ake bashi.

Kashe-kashen Zamfara: Masu rike da mukaman gwamnati na nuna wa juna dan yatsa

Kashe-kashen Zamfara: Masu rike da mukaman gwamnati na nuna wa juna dan yatsa

Ya yi misali da jawabin da Ministan cikin gida, Abdulrahman Dambazau ya yi a wajen taron yan jarida na kasa da kasa karo na 67 da akayi a Abuja.

"Ba mu da wata jiya bayan Zamfara saboda haka dole mu hada hannu mu gyara ta. Kamar yadda gwamnatin tarayya ta fadi, nima ina ganin laifin gwamna bisa yadda ya ke sakwa-sakwa kan batun kashe-kashen da yan bindiga keyi a Jihar," inji Marafa.

Mr Dambazau ya yi kira da gwamnoni su mayar da hankali wajen magance matsalolin da ke adabar jihohin su maimakon kokawa da gwamnatin tarayya ko hukumomin tsaro.

"Shugabanci na gari ne zai magance duk wasu matsaloli da ake fama da su a sassan kasar nan, muddin akwai shugbanci na gari, duk wadannan matsalolin ba za su taso ba," inji shi.

A wata sanarwa da ya fitar, Marafa ya ce mataki na farko da za'a dauka wajen kawo karshen kashe-kashen shine gwamna ya jajirce ya bincike na kusa da shi da ake zargi da hannu cikin kashe-kashen kuma ya hukunta su idan an same su da laifi.

"Mataki na biyu kuma shine gwamnan ya mayar da hankali a kan ayyukansa, ya dena tafiye-tafiye zuwa Abuja da kasashen waje don ya samu sukunin yiwa al'ummarsa shugabanci na gari," inji shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel