Ta tonu: Wasu dalibai mata a jami'ar Bayero su fallasa yadda malamai ke neman yin lalata da su

Ta tonu: Wasu dalibai mata a jami'ar Bayero su fallasa yadda malamai ke neman yin lalata da su

A wani shiri da gidan yada labarai na BBC ke yi na Adikon Zamani, sun wallafa wata fira da wakiliyar su tayi da daliban jami'ar tarayya ta Bayero dake jihar Kano inda suka labarta mata yadda wasu malaman jami'ar ke neman yin lalata da su.

Kamar yadda daliban wadanda aka sakaya sunan su a firar, daya daga cikin daliban ta bayyana cewa hakan ta taba faruwa da ita lokacin da wani malami ya nemi yayi lalata da ita kuma da ta ki amincewa sai yayi mata barazana na kada ta.

Ta tonu: Wasu dalibai mata a jami'ar Bayero su fallasa yadda malamai ke neman yin lalata da su

Ta tonu: Wasu dalibai mata a jami'ar Bayero su fallasa yadda malamai ke neman yin lalata da su

KU KARANTA: Ziyara Bayelsa: PDP ta tozarta Atiku

Legit.ng ta samu cewa wani namiji da aka yi fira da shi shima ya bayyana cewa ya taba shiga matsala sakamakon alakar sa da wata daliba da malamin ke so a ajin su.

Sai dai wasu daliban sun bayyana cewa idan dai har malaman na da laifi to suma matan na da nasu laifin domin wasun su sune ke baiwa malaman damar da har za su nemi suyi lalatar da su.

Da yake mayar da martani, shugaban sashen jin dadin daliban jami'ar Dakta Shamsudden Umar ya ja hankalin daliban da su rika fallasa dukkan irin bata-garin malaman ga hukuma domin daukar mataki.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel