Cin kofin duniya: 'Yan Najeriya sun fiddo Ahmad Musa takarar shugaban kasa a 2019

Cin kofin duniya: 'Yan Najeriya sun fiddo Ahmad Musa takarar shugaban kasa a 2019

- Wasu 'yan Najeriya tuni suka fara nuna sha'awar su na cewa Ahmad Musa ya zama shugaban kasar Najeriya a 2019

- Wannan dai ya biyo bayan kokarin da dan wasan yayi akan kasar Iceland jiya

- Ahmad Musa ya zura kwallaye 2 ne a ragar kasar Iceland bayan dawowa daga hutun rabin lokaci

Wasu 'yan Najeriya tuni suka fara nuna sha'awar su da cewa fitaccen dan wasan gaban nan na Najeriya Ahmad Musa ya fito takarar shugabancin kasar a 2019.

Cin kofin duniya: 'Yan Najeriya sun fiddo Ahmad Musa takarar shugaban kasa a 2019

Cin kofin duniya: 'Yan Najeriya sun fiddo Ahmad Musa takarar shugaban kasa a 2019

KU KARANTA: Wata budurwa a Fesbuk ta gogawa wani kanjamau

Wannan dai ya biyo bayan kwazon da dan wasan yayi a karawar Nijeriya da kasar Iceland jiya inda ya zura kwallaye biyu ringis a ragar abokan hamayyar.

Legit.ng ta samu cewa sai dai gama kwallon keda wuya sai kawai jama'a suka fara tallata dan wasan musamman ma a kafofin watsa labarai inda suka nuna sha'awar ya jagoranci Najeriya a 2019.

Wasu 'yan kasar dai sun bayyana cewa a cikin shekaru 3 da shugaba Buhari yayi yana mulki bai faranta masu rai ba kamar yadda Ahmad Musa ya faranta masu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel