Hukumar 'Yan sanda ta kori jami'ai 19, ta rage mukaman 9 a jihar Ogun

Hukumar 'Yan sanda ta kori jami'ai 19, ta rage mukaman 9 a jihar Ogun

A ranar Juma'ar data gabata ne hukumar 'yan sanda reshen jihar Ogun ta bayyana cewa, ta sallami wasu jami'an ta 19 a tsakanin Yulin 2016 da watan Yuni na shekarar nan sakamakon laifuka daban-daban da suka aikata.

Hukumar ta kuma bayyana cewa, ta zabge mukaman wasu jami'an ta guda tara yayin da ta dauki tsauraran matakai kan wasu 11 a tsakanin wannan lokuta.

Kwamishinan 'yan sanda na jihar, Ahma Iliaysu, shine ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a shelkwatar hukumar ta Eleweran, inda ya bayyana cewa akwai wasu jami'ai hudu da ta gurfanar gaban Kuliya bayan sallamar su daga aiki.

Hukumar 'Yan sanda ta kori jami'ai 19, ta rage mukaman 9 a jihar Ogun

Hukumar 'Yan sanda ta kori jami'ai 19, ta rage mukaman 9 a jihar Ogun

Iliyasu ya bayyana cewa, hukumar ta dauki wannan hukunci ne kan jami'an domin ya zamto izina ga sauran al'umma da zai tabbatar da cewar jami'ai kansu ba su tsira ba yayin da suka sabawa doka.

KARANTA KUMA: Hukumar 'Yan sanda ta tanadi Jami'ai 5000 da Makamai domin Gangamin APC a Garin Abuja

Kwamishinan 'yan sandan ya kuma jagoranci jami'ai wajen cafke wasu 'yan ta'adda 25 da suka hadar har da Murtala Babatunde da Taiwo Rasaq da ake zargin su da yiwa wasu dalibai biyu na jami'ar Olabisi Onabanjo kusan gilla kuma suka binne gawar su cikin dokar Daji.

Legit.ng ta fahimci cewa, a yayin wannan sintiri da hukumar ke gudanawar domin fatattakar masu aikata miyagun laifuka, ta samu nasarar kwakulo wasu muggan makamai masu hadarin gaske a cikin birnin na Abeokuta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel