Shugaba Buhari ya sake sabbin nade-nade a Gwamnatin sa

Shugaba Buhari ya sake sabbin nade-nade a Gwamnatin sa

A ranar Juma'ar da ta gabata ne Shugaban Kasa Muhammadu Buhar ya bayar da lamunin sa na nada wasu sabbin mutane hudu masu gudanar da al'amurran babban bankin kasar nan da kuma wasu sabbin shugabanni biyu na wasu ma'aikatun gwamnatin tarayya.

Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya bayyana, shugaba Buhari ya kuma sabunta wa'adi na mukaman wasu shugabannin ma'aikatu uku na gwamnatin tarayya.

Sabbin nadin mukaman sun hadar da na Adeola Adetunji a matsayin Darakta na babban bankin kasar nan na wa'adin tsawon shekaru hudu da ya fara daga ranar 7 ga watan Yuni.

Sauran wadanda suka samu nadin mukaman a babban bankin kasar nan sun hadar da; Farfesa Mike I. Obadan, Farfesa Justitia Odinakachukwu Nnabuko da kuma Farfesa Ummu Ahmed Jalingo duk na tsawon wa'adin shekaru hudu da tasirin sa ya fara daga ranar 7 ga watan Yuni.

Shugaba Buhari ya sake sabbin nade-nade a Gwamnatin sa

Shugaba Buhari ya sake sabbin nade-nade a Gwamnatin sa

Shugaba Buhari ya kuma nada Farfesa Abdullahi Dasilva Yusuf, a matsayin babban Likita da zai jagoranci Asibitin koyarwa na Jami'ar Ilorin inda tasirin wa'adin sa zai fara daga ranar 19 ga watan Yuni har zuwa tsawon shekaru hudu.

DUBA WANNAN: Mutane 6 sun yiwa wata Yarinya Fyade har Lahira a Jihar Anambra

Hakazalika Shugaban kasa ya nada Dakta Pauline N. Ikwuegbu, a matsayin sabon shugaban kwalejin gwamnatin tarayya ta Eha-Amufu dake jihar Enugu, inda tasirin wa'adin sa ya fara daga ranar 19 ga watan Maris har zuwa tsawon shekaru hudu.

Legit.ng ta fahimci cewa, Olusegun A. Adekunle, Sakataren dindin a Ofishin Sakataren gwamnatin tarayya shine ya bayar da wannan sanarwa da ya bayyana cewa, Shugaba Buhari yana sa ran wannan mukaman za su zamto kira zuwa ga yiwa kasa hidima inda yake shawartar su akan jajircewa kan gaskiya da rikon amana wajen sauke nauyin da rataya a wuyan su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel