Buhari: Ba zan manta da lokutan wahalar 'yan Najeriya ba

Buhari: Ba zan manta da lokutan wahalar 'yan Najeriya ba

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar wa da daukacin al'ummar Najeriya cewa, gwamnatin sa ba za ta taba mantawa da lokutan wahalar su ba da kuma tagayyara inda yace zai ci gaba da aiki tukuru domin daɗaɗa ma su da inganta tsaro.

Yace gwamnatin sa za ta kara kaimi wajen dawo da zamantakewa da alkaryu na yankunan da 'yan gudun hijira domin gaggauta komawar su lafiya cikin kwanciyar hankali.

Cikin wata sanarwa da sanadin kakakin fadar shugaban kasa Mista Attah Esa, da ya bayyana cewa shugaban kasar ya bayyana hakan ne a ranar Juma'ar da ta gabata da sanadin kakakin sa Mallam Garba Shehu, da ya karbi bakuncin 'yan gudun hijira a fadar Villa a madadin shugaba Buhari.

Buhari: Ba zan manta da lokutan wahalar 'yan Najeriya ba

Buhari: Ba zan manta da lokutan wahalar 'yan Najeriya ba

Shugaban kasar ya taya murna ga 'yan gudun hijirar kimanin 2000 na sansanin Kuchingoro dake garin na Abuja da suka shirya tsaf domin komawa alkaryar su dake yankin Arewa maso Gabashin kasar nan.

DUBA WANNAN: Mutane 6 sun yiwa wata Yarinya Fyade har Lahira a Jihar Anambra

Ya yi godiya da jinjina ga al'ummomin kasashen ketare da na Najeriya ciki har da Aliko Dangote, Janar T.Y Danjuma da sauran masu jin kai da suka malalar da dukiyar su domin taimako na sake ginawa da farfado alkaryoyin da aka rushe cikin yankunan Arewa maso Gabas.

Misis Maryam Nuhu, jagoran 'yan gudun hijira da mata ne kadai da yara, ta yabawa gwamnatin shugaba Buhari dangane da cin galaba akan 'yan ta'adda na Boko Haram da kuma sake gina alkaryoyin su da aka rusa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel